Tuesday, 28 June 2016

SABEER


Abakin rijiya take zaune ta zabga uban tagumi hawaye na kwalala a idanunta na iso wajen cikin hanzari nace hava indo meye haka yanxu har naje nadawoo baki kai ruwan naki ba meyasa kikeson daura wa kanki damuwa ne ta dago kai ta kalleni tace raliya bazaki gane halin danake ciki bane wallahi SO CUTA NE, kawai sai na kwashe da dariya domin maganar ta kenan,raliya bazaki taba gane halin danake ciki ba sai randa kika fara soyayya  bazaki fuskanci kalubalen rayuwa ba sai kin fara soyayya kibarni kawai naji da matsalata sai nace hava indo dauki ruwanki mutafi kar goggo ta nemeki kinga al muru takawo kai za'ayi ma na fada

 Sun dauki ruwa suna tadi sai raliya tace idan har audu na sonki da daske yaci ace yadawoo gareki bawai yatafi ya manta dake ba hmmm raliya kibari kawai,toh ke ya maganan naki kun dai dai ta da salisun ne hmmm lalle ma indo kina magana kina manta waye raliya ai kuwa tunda nagama primary bani da gurin komai sama dana karasa karatu na wannan ai duk shirme ne wani soyayya to ku tattabaran me kuka samu sai suka kwashe da dariya.......


Auzubillahi minal shaidani rajim hava mallam baka da ido ne zaka bige ni ka wuce kamar ka bugi dutse shi kuma bai yi magana ba yaci gaba da tafiyarsa tace kai mallam dakai nake sai indo tace ke inna masifa mahaukaci ne fa sai taja baya hhhhh indo dagaske 😳 wallahi ni kinga tausayi yake bani baya magana sai tsince tsince ALLAH sarki ALLAH yabashi lafiya sukace amin suka wuce.

Ahaka suna hira har suka iso gidan su dayake makwabta ne wata guntun zana ne a tsakanin su aiko indo na shiga gida Goggo  ladi tahauta da masifa akan ta jima abakin rijiya ina jinta tana ta rantse rantse wai layi hmm tinanin audu dai nafada a raina sai baba zuwaira tace raliya ki daura mana abincin dare saboda yau ummah tana dan jin zazzabi nace toh baba nashiga magirkin mu najiyo indo tana ta raira waka wa audu sai na leka nace ke tattabara uwar soyayya kullum sai kinsha kona mana abinci akan Audu raliya kishiga hankalinki kagama girkinki yau xamuje dandali tabdi ni sai dai naje nayi bitar karatuna toh bakomai ki gama tukunnan.

 Misalin karfe 8:00 na dare matasa da yam mata anfita dandali  raliya da indo ma sunzo anan taga wasu daga cikin abokanan audu tace kinga su buba can natafi najiyo labarin audu  raliya taja wani dutse tace kinga zamata anan.
 Tana zaune tana waige waige sai ta hango wannan mahaukacin sai tadauki takardunta tabi indo anan ta lallabata suka kama hanyar gida sai indo tace uwar karatu yau ya akayi da wuri haka sai nace wallahi naga mahaukacin dazu ne nikuma ina jin tsoronsa sukayi ta hira har suka isa gida.
 Anan suka kafa hiransu a kofar gidansu indo,indo tace hava audu son dakake yimun yasa na zauce nazama kamar bani da cikakken hankali a kanka gashi raliya ma na mun kallo mara aikinyi. Sai nace hava indo walhi ki fahimceni bahaka bane sai tace to yaya ne raliya ?  Hmmn

WAYE AUDU??......
 Audu shine gwarzo kuma jarumi acikin samarin kauyen nafada dake kasar gombe kauyen ba babba bane amman akwai mallamai da rufin asiri audu dan kanin limamin garin ne wato mal dauda hamza kanin mal ahmadu hamza limamin garin,mal dauda yana da yara biyar audu na farko sai tasallah,hamza,sai yan buyu Hassan  da Hussain.

 Audu ya zama mai farin jini sanadiyar jazama da gidansu ke dashi sannan mahaifiyar sa yer niger ce hakan ya hada masa kyau dakuma kwar jini
  Mallam dauda mahaifin audu matar sa daya ne hamsatu suna kula da tarbiyyan yaransu sosai,audu kuma ya kasance mai hazaka a gurin karatu da farauta yana bin mahaifin indo zuwa farauta lokaci zuwa lolaci dayake mahaifimta ne babban dan farauta agarin
 Shikuma audu anan ya kulla aniyar auren indo a ransa kaf karkarnsu babu wanda bai san audu da indo ba komai nasa indo itama komai audu soyayyarsu tayi karfi sosai
Kwatsam akayi bako daga niger dan uwan su mamar audu yace shi zai kai audu makarantar boko a niger ahaka suka tafi duk da karshen time yana zuwa amman wannan karon abun yaci tura domin sai sakon gaisuwa yake aika wa yan gda da kuma indoo........
 WAYE RALIYA??
Mahaifin raliya salimu sani tare da mahaifyarta Zainab  sani sukazo garin nafada da cikin  garba sun samu hadarin mota ne kansu ya juye sun zauna agidan limamin garin na tsawon wata shida sun dan samu lafiya amman sunkasa gano daga ina suke hakan yasa mai gari yabarsu dasuci gaba da sabon rayuwa anan anq haka aka haifi raliya, daga nan sai mai gari yace muddin zaici gaba da zama a girinsa to ya auri yersa ahaka ya auri zuwaira yer mai gari amman suna zaman lafiya da kwanciyan hankali duk yan matan garin na gudun mu amala da raliya amman bnda indo haka kuwa garba bashi da aboki sama da Bashir  yayn indo.
  Ahaka suke rayuwarsu sai dai shi Salimu sani bai yarda yaransa suyi rayuwa ba karatu ba dukansu suna kishin karatu ahaka kuwa garba yatafi kasar kano neman ilmin boko itakuma raliya bakinta primari ne kawai.

INDO kuwa yar mallam haruna ne babban masu farauta na kauyen su mallam haruna yana da yara hudu maza biyu mata biyu bashir dan fari sai sadiq sai aisha watau indo sannan talatu. matar sa guda daya mamar talatu wato Goggo  daso domin maman su indo  ALLAH yamata rasuwa da jimawa tun indo tana jaririya,Goggo  take wahalarsu har su ka kai haka.
 
Indo kizo inji Goggo  talatu ne takirata sai nace bakomai kawata kije sai naxo bari naje gurin ummah don tana dan zazzabi ALLAH yabata lafiua amin suka watse
 Akwana atashi yau audu ya shafe shekara batare da dawowa ba indo tayi jinya har ta hakura  akoda yaushe sai dai ta zauna tayi ta irgen zaman ta batare da audu ba raliya kuwa tun abun na bata dariya har ta koma tausayawa aminiyarta.
 
Ayau litinin garin nafada tayi babban rashi wato limamin garin ALLAH yayi wa rasuwa baffan su Audu  akayi jana izansa akayi uku akayi bakwai duk audu bai zo ba,sai indo suka shirya da raliya zuwa ta aziyya a gidansu audu.
 Sukaje bayan sun musu ta'aziyya sai suka koma gefe anan suka ga saddiqa yariyar liman suka masa kusa da ita nace ina wuni saddiqah shuru saddiqah ya hakuri?? ALLAH ya jikansa da rah........... daas ta wankawa indo mari

Saddiqah meta miki rufe min baki raliya yer matsiyata mayu marasa asali,wani kunkurun takaici ya makale mun awuya nace indo tashi mutafi toh idan ba tafiyar  ba mezakuyi eh mayya indo duk kin rike mana zuciyar dan uwa yanxu akanki kinsa yaki danginsa shegiya matsi....

Keh! Saddiqah ya isheki  inji indo shiru shiru ba tsorobane gudun magana ne mara tarbiyy........dasss mamar saddiqah umma laddo ta kwashe tq da mari. Kawai tafita da gudu raliya ta bita bata nufi ko ina ba sai bakin rafi raliya tabita ta kamata Kibarni kibarni raliya inji da rashin uwa ko masoyi ko da masifar yan uwansa rayuwatq bata da amfani kawai ta fashe da kuka kiyi hakuri ALLAH yana sonki bai ki ki ba. Tabbas ALLAH yana sonku dukanku tunda banzo da bulala na ba muryan ya doshi kunnensu dukansu zuciyar raliya ya tsinke lokacin data rasa sanin dalili indo kuwa hawaye cak ta tsaya amman ta kasa dago kanta sai yace indo ta audu ikon ALLAH  Dga kan da zatayi taga wani matashin saurayi sanye da kananan kaya yana watso mata murmushi sai ta sankare tasan wannan  mai kama da audun ta ne sai ya durkusa dab da ita wani kamshin tulare ne ya ratsata
 Hmm raliya na haukace magananki gaskiya ne bani da hankali kiga audu na mun gizo a shigen yan  birni tajuyo taga raliya bata hankalinta.

Raliya!Raliya!!Raliya!!!
Na’am kina ganin abinda nake gani,kwarai indo nima kin raba mun haukan naki.
Shshsh Indoh wani zazzakar murya ne yasake tashi indo ta lumshe idonta takalleshi yasake matsowa dab da ita yakama hannayenta duka biyu hmmm tun yaushe indo ta tafi duniyar tunani tana ganin wannan mafarki ne saboda tasan Audu  bashi da dabiyar taba jikin mace balle ma indo matar da ko kuda namiji bayaso yatabata tab wannan abun da abin al'ajabi my love tunanin me kikeyi am urs Abdoul  kibide idanunki ki kalleni masoyinki ne... INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN dukan mu muka dago muka zuba wa sarautar ALLAH ido saddiqah ne rike da kugu yaya audu yanxu kazo ka gari amman ka kasa isa gida zaka tsaya agurin karuwan nan,a gigice ya dago kansa ya ce saddiqah waye karuwa kinsan me kike fadin ya wanketa da mari taruga da gudu wallahi saina gayawa abba yadau jakarsa ya bita agigice sai yanzu indo tasan ba mafarki takeyi ba sai dai ranta fal cike yake da farincikin dawowar masoyinta gareta raliya ta katse mata tunani tace tashi mutafi kawalli
 Lalle audu ya kara kyau daman haka birni yake tare inji indo kwarai kuwa nakoya a social studies ruwan su na birni yafi namu sannan abinci su dama komai da komai suka isa dai dai bishiyar maina kofar gidansu suka zauna indo kinsan yau abinda yafaru yabani mamaki wallahi raliya wai daman saddiqah son audu takeyi ne komai..tabbas sonshi takeyi indo kiga wani zakewa data keyi akan kuwa hmmmm lalle idan har hakane ni Aisha indo ina da jan aiki agabana domin kuwa nasan halin ummah laddo aaaa wallahi kawalli baki da wani sauran fargaba tunda ke kike mulkin zuciyar Audu wani sanyayyar murmushi indo tayi tace sai mu dage da addua

Audu ya isa gida ya tarar da su abbah akofar gida bayan sun gaisa yanemi izinin isar da kayan cikin d
Gidan, ai ko yana shiga ya tarar da siddiqah tana kuka ana tambayan ta tana kora jawabin karya da gaskia,tasallah ta rugo da gudu yaya audu oyoyo dagaske fa take yazoo kai yaya audu ta amshi jakansa tayi dakinsa ta ajiye tafito  mamarsa tafito da farinciki ta tare danta audu ya mutan zender lafiyansu kalau ku kawo masa ruwa aka kawo yasha sai ya juya umma laddo ina yini yakuma muka ji da hak.......mari daga gun ummah laddo uwar ka ne mara tarbiyyya wanda baisan me yakeyi  ba sai ta kama kuka da kururuwa irin na jahilai mata (wannan bayi bane yan uwana mata mukula)
 Dayake duk agida daya suke amman kowa da bangarensa sai yakoma side na mahaifyarsa ya zauna yana karatan wasikar jaki....

Sai yaga hankan bamai yuwa bane sai yatashi yatafi gurin mahaifinsa a bakin kofar gidan su suna karban gaisuwa. Karan wayarsa tafara ringing wakar adam a zango na (aeesha aeesha mai daria indoh!) Sai yadauka hello Hoozaif  na isa lafiya ina gida toh ALLAH yajikan sa amin ga fiddy matana gaida kai sai ya katse wayar. Ai kuwa yasake kira yane abokina ka katse network toh fiddy na gaisheka ina amsawa wai nabata ku gaisa excuse me plz am wit my elders ok friend bye k.......

Abangaren indo kuwa murna da zumudi yacika mata zuciya farinciki ba iyaka sai dai inta tuno da saddoqah abin yana firgitata akasha wankq tahau wani atqmfarta mai kyau aka ci ado duk tabi ta rame tana tsaye agaban mudubin dakinta tace hmm na kusa murmurewa nasan dahaka yau ana bakin mudubi raliya na ta dariya ke meye haka sai suka tafa suna dariya daka gansu kaga walwala a tattare dasu.......

Bayan sallah isha yaro yashigo ina yini Goggo  wai Audu  ne yakeso amasa iso zuwa gurinki zai gaidaki Goggo  ta tashi oh Audu wa sannu da zuwa lqle marhaban bakin birni ya iso Goggo  ina wuni,lafiya lau dannan ya gida ya jama'a ALHAMDULILAH ya hanya ya kabaro mutanen zender lafiyan su kalau goggo yayi kyau  sai yadau leda ya mika mata raliya da indo na gefe suna ji sai ya fita aiko tuni suka bishi suna ta godiya.
Ta tarar dashi a soro nq gidan yace swt indo tace naam masoyina toh kun fara kar ka manta a gidan sirki kake kuma ga abba can a kofa awwwww inji audu sai yace raliya kimin iso gun su umma in gaidasu....
 Gaskiya hakan  bakaramin dadi yamata ba suka wuce sukaje suka gaida yan gida suka fito sai yadau leda yace tsarabarku da yan gidanku takai ta dawo gunsu sai tace indo ni zan koma aaaa inji audu muje dandali dai yau muyi hira suka kama hanya suna tadi sai sukaji ana cewa raliya, indo juyawan dazasuyi wani abin al ajabi ne wai mahaukaci da magana harda sanin sunan mu ya iso kai xan yankaku hahaha kene matana yanuna indo kai ne abokina ke kuma kishiyata sai audu yace wannan fa sai indo tace wannan mahaukaci ne yajima agarinnan da ba ya maga ma amman yanzu ya fara ALLAH SARKI,ALLAH ya baka lafiya sai yace kaima haka,hmm sai Audu  yace meye sunanka kaima haka toh KAIMA HAKA! toh katafi wasa aa bazani ba sai da indo aaa kai nabaka raliya itace matarka indo matatace kaga ai indo kishiyarka ne eh hakane fa hhhhha amman tana hararana waye matana mana toh kinji ki daina sai indo tace kawata sabn kamu sai suka wuce sai yace sai da safe sukaje dandali.

 Suka matsa gefe indo kuwa na bitar karatun allon ta sai dai indo taga sababbin canji a tattare da audu..... Audu data sani da kunya amnan yanxu daf da ita yke hira abun ya mugun daga mata hankali(kirana gareku yam mata kar zuman so ya debeki kikasa ganin laifin saurayi idan yayi tsawatar masa ALLAH yasa mu dace ameen)

Acan zender kuwa fiddy takasa zaune takasa tsaye saboda tashin hankalin rashin ganin audu(abdoul) idan ta kirashi baya picking ta  koma gurin Hoozaif, Hoozaif  plzz save my life i can do without Abdoul  zan iya rasa raina fa hava fiddy meye haka kamar ba mace ba kin makale wa mutum yana gudunki, kina da num nasa kije sauran yarage miki
Ta dago wayanta mai kiran iphone 7 ta kira shi yayi dai-dai da lokacin da audu yake koya wa indo da raliya karatu a bayan gari ga kaima haka ma yana dan tsince tsincensa da surutunsa sai wayarsa ta hau kara sai ya dauka yace hello hi my love inji fiddy hava Abdoul  ba kyau wulakanta bani Adam,look lady i told u indo is my wife to be so dont ever try to distroy me
Hhhhhhhh sai ya katse fushi ta bayyana afuskarsa karara sai indo tace meye faru masoyina?

Indo babu! kawai maganan makarantar mu ne sakamako na baiyo kyau kamar yanda nake bukata ALLAH sarki  ALLAH ya sa ka dace mijina…..
(A esha ae sha mai kwalliyya indo!) Wayarsa ne take ruri ya dauka hello Hoozaif  yakake?bana kalau saboda fiddy ta fadi ta suma... akan meyasa sai yatashi ya matsa gefe aboki meya sameta cux ka wulakanta ta man aaa watsa mata ruwa sai ya kashe yakira su sai Hoozaif  yace gata hello Abdoul  naam fiddy plzz forgive me i dont mean to hurt u wallahi i do my  dear uhm take care fiddy baby
 Woow tayi tsalle Hoozaif  ka iya target nagode xakaji alert yanxunnan tacire wayarta tace bani acc naka kwaram yaji alert 50k woow fiddy u r too much tanxxx u alot bakomai dis just the beginning.

 Acan bangaren su indo kuwa raliya zuciyarta cike fal yake da mamaki domin ta tsince wasu kalaman audu shikoh sai zuba soyayyah suke yi da indo .......

 Indo acikin kankanin lokaci ta murmure ta washe sai dai damuwar ta ita yawan kiransa a waya da ake wanda ta fahimci mace ce amman yace  yer dan uwansu ne.
Sai kuma saddiqah umma laddo ta dage akan sai ya auri yer ta.

Kwana atashi bawuya gurin ALLAH gobe arba'in na mal Ahmadu hamza hakan yayi dai~dai da zuwan wata mata gurin mai gari tace mai daya nema mata wata yarinya budurwa domin ta rinka tayata aikatau ana biyanta sannan za'a saka ta a makarantar book acan birnin tarayya abuja  mai gari yatara iyayen 'yan matan garin yamusu bayani kamar haka

 Toh mutanena bazan taba kusantar abinda zai cutar daku ba nasan Hajiya Rukayya ciki da bai domin ni Dan dakin mahaifiyarta ne toh duk Wanda ya amince yaba da yersa ga ita na tabbata zata rike amana Amman kuje kuyi shawara da anufi na adau saddiqah yer mallam ahmadu Amman yakagani mal dauda??
Eh toh bari naji na bakin mahaifiyarta sai baban raliya yace ita ta dace domin   marainiya CE kaga anshuka khairin ga ahalin marigayi ALLAH ya jikansa sukayi fatiha suka watse
 Rannan litinin da safe akayi adduan arba in sai dai laddo taki amincewa da akai yerta akan haka har husuma takusa barkewa da kyar aka kulla bakin zanin
Mai gari beji dadi ba don haka yasa aka kira mahaifin raliya yaji ta bakinsa ana magana kuwa ya amince dayake surkinsa be
Sai dai baisan ko yer tasa zata amince ko bazatayi ba..

Ya iso gidansa ya kirawo su matansa da ita raliya ya zayyana musu abinda suka yi budan bakin Maman raliya tace mallam duk abinda ka sa akan my dai dai ne domin nasan bazakasamu ahannun da bashi da kyau ba gurin mu kawai raliya tasamu ilmin boko Dana muhammadiyya ..........
Gaba daya naji jikina yayi sanyi zanbar inda nasaba hawaye ta kubuce min sai baba zuwaira tace hava mallm Ku tsaya kuji ta bakin yarinyar tukunnan Ku yanke hukunci sai yace raliya nace naam Abba sai yace kin amince nace eh Abba sai yace kukan me kikeyi nace rabuwa da mazaunina........
 Yace ALLAH SARKI sabo turkin wawa kidaure hakan zai baki damar cimma mana gurin mu na rayuwa domin zakiyi karatu boko da na islamiyya,Abba ba komai na amince suka hada baki ALLAH ya miki albarka raliya ameen Abba natashi nashiga ciki...........

Abba yasanar da maigari, mai gari yayi farinciki sannan yace za'a hadasu da zuwaira dakuma Audu suje suga inda aka ajiyeta babanta yayi farinciki sosai
Mai gari ya shiga gida yagayawa hajiya Rukayya abinda akayi tayi farinciki sannan sukaje gidan su malam salimu tare da Maman zuwaira talaa domin a fahimci juna sukaje suka tattauna sannan tace tana biyan dubu goma a wata sai mal salimu yace Hajiya idan har xaki kula da tarbiyyanta kibata ci da sha sannan ki sakata a makaranta toh wallahi kibar albashi yace AAA mallam haqqi Nada wuya nidai nafita nabarsu suna ta tattaunawa...........

Na nufi gidan su indo naje akace ta fita kawai na doshi bakin rafi nasan suna can ita  da Audu INA tafiya ina ta hiran zuci kawai sai naji an tsoratani Dana firgita sai yace matana hmmm ashe Kaine eh nine matana mai katon kai, sannu sai nayi murmushi nima xan biki  sai nace muje yagudu yadawo yana tayi ...............
Na Isa dai~dai rafi nagansu suna hira sai na tsaya ina kallon su sai suka juyo nace tattabaru sai indo ta cilleni da dutsi na gauce muna ta dariya nazo kusa da su sai hawaye ya yanke mun nafara kuka gaba kidaya hankali indo yatashi haka kuwa Audu ma yace indo meya faru sai nace yaya Audu ina hajiyar nan wai zata tafi birnin tarayya domin na mata wasu ayyuka sannan zata sakani a makarantar boko kawai indo tafashe da kuka ta rungumeta suna  ta kuka Audu ne yayi ta maza yace nasan da tafiyarki domin ance nida baba zuwaira zamu rakaki hava sai sautin kukan indo yakaru  wani abin mamaki saida Audu yajuya Yaga wannan mahaukacin na hawaye sai yace indo kuga ikon ALLAH su sake juna suka juya gurin  Kaima haka sai Abdoul Yakama hannunsa  anan Yaga anrubuta samha da razor sai yace kuga wani ikon ALLAH  sai sukace ko wayene oho sai yace kaima haka yace naam meyasa kake kuka yace bazan fada ba sai yace kafada sai yace cinnaka nane ya mutu yau ake sadakan Dari ...........
 Duk sai suka rushe  da daria sai shima yatashi ya gudu sai indo tacire wani zobe a hannunta tasa a hannun aminiyarta suka sake sabon kuka Audu yace ai Baku Rabu ba kuna tare.

 Rannan Asabar da sassafe suka shirya domin tafiya abuja haj Rukayya  da raliya sai zuwaira da Audu Maman zuwaira taso kukq sai dai dazaran tayi kuka raliya xata karaya don haka ta jure tana yake suka hadu abakin kofan mai gari sai dai ba aga raliya  ba domin tafita tana kuka sun zata taje gidan mai gari ne
Sai magari yace ina raliya sai akace watakila tana gidansu indo ana shirin tura dogari sai aka hango Audu  da indo suna zuwa tana rike da jakansa tana kuka sun iso gurin akace ina indo duk sai sukayi shiru sai indo tace ai bataje gidan mu ba sai suka hada baki to ina taje😳 sai maigari yace ko batason tafiyane ta gudu sai mal salimu yace aa baza tayi haka ba sai Audu   yace nasan inda take ina zuwa sai ya juya aguje haka indo ma tabi bayansa sukaje suka taddata agurin KAIMA HAKA yana zaune ita kuma tana ta kuka tana jingine da wani bishi sai audu ya iso yace raliya meya faru tace yaya Audu  bana son barin garin  nan nasaba daku wallahi dabadan bana son saba wa mahaifina ba dana buya kizoo mutafi inji indo su abba suna jiranki.......

Suka kama hanya sai tace kaima haka sai yace matana, sai tace saduwan alheri sai tafara gudu tayi bakin fada tasamu iyayenta tana ta kuka sai Haj ta kama hannunta suka saka kayanta amota suka shiga indo kam kuka kamar zata sume haka kuwa raliya kai duk mai tausayi idan yagansu sai yayi jimami mai gari kansa sai da yayi hawaye..........

 Suka dau hanya suna ta hira    Audu kuwa sai tausan raliya yakeyi da tausasan kalamai mai kwantar da hankali a haka har huce tafara daria suna ta hira bello driver sai tadi yake  musu na barkwanci suna ta daria......
A bauchi sukayi breakfast oh ALLAH tafiya mabudin ilmi inji Mahmoud nagudu lalle yau ni raliya nai nisa mun karya awata hotel sannan muka dau hanya  muna tafa misalin karfe 6:39 muka Isa gidan Hajiya rukayya dayake gwarumfa wai daula na zuba kai nayi kallo sannan nayi kauyanci daula na magana wato da bazan iya muku kwatancen ya gidan yake ba sai nahuta saboda nagaji......
Haj mai fara a ta shigardamu side na baki aka kawo mana abinci irin dabn daban sannan
   Tace ga ban daki muyi wanka hmmm karku ga yanda nida baba zuwaira mukayi kauyanci sai da wata tazo ta nunna mana mukayi wanka mukayi  sallan isha sannan Hajiya ta bukaci da muzo parlour mu tattauna mukazo tace bazan tsauwala raliya ki rikeni kamar mahaifiyar ki nima xan rikeki tamkar yayinyar da na Haifa  anan suka fahimci juna sosai sannan suka watse da zummar gobe zasu koma nafada sai dai Hajiya tace subari sai jibi

 Acan bangaren indo kuwa abinci ta kasa ci tasaba ta dau kukanta takai wa raliya Amman yanxu ba ita ba Audu sai ta kwanta tana kuka har barawon bacci ya sace ta..........
Haka raliya tana walwala Amman dataxo kwanciya ta tuna da indo ta rinka kuka har gajiya yasa ta yi bacci
 Washe gari da safe muka sha farfesun kifi da burodi  da shayi wai sai da na tuna da yan gidan mu da indo tab rabon danaci kifi tun dawo war yaya garba daga kano ALLAH sarki YAYANA wata hawaye ta gangaro min na goge
 Washe gari dasafe su baba zuwaira da Audu  suka shirya komawa hmm lalle sanin yakamata sai dan asali wato hajiya mota tabada a maidasu har nafada sannan ta musu goma na arziki...

Sukatafi muko muka dawo gida cikin gidan anan hajiya ta nuna min kan gidan sanan tace aiki na shine share mata daki da gyaran gado sannan zan zama dai kamar personal asistance nata, sanan tace kamal dan mai gida nane shida kaninsa faisal mahaifiyarsu tarasu da jimawa sai dai kiyi hakuri da miskilanci kamall,yanxu basa nan suna katsina gun dagin mahaifiyarsu sun je hutu, sannan yarana  biyu ne gaba da baya amman dayan yayi aure da wata uku yayi hatsarin mota ya rasu danaga idon Hajiya  duk ya cika da hawaye tace shine yaron danake so domin biyayyar dayake min sai nace ALLAH yajikansa da rahma tace amin taja wani abu ta goge idonta sannan tace sai kuma mace ita kuma tana  karatu zata iya dawo wa ko wani lokaci muna kiranta mummy domin taci sunan mahifiyar ALHAJI
Sharuda na shine akwai wani daki da ba a shiga a gidan nan sanan banason kazamta da fatan kin gane kuma zaki bani hadin kaii nace eh Hajiya  insha ALLAH sai tace akwai bilkisu itakuma yer kanwatane,yanxu haka tana kano tana karatu amman intadawo anan gidan take saboda suna dayawa a gidansu nace to Hajiya  tacee aaa raliya ni fa kamar uwace a gareki kina kirana da maamaa kiran da yaran gidan  nan keyi mini kenan nace toh maamaa...
 Tashi ki shirya muje kirakani kasuwa kinji nace to natashi nashiga dakin da aka ware akan nawane nasaka wani atamfar da yaya garba yasaya min nadau jan baki na gwabza kulliyana danake ji kure adaka ne nafito sai hajiya tace har kin shirya nace eh tace aa aje agoge wannan dankwale dankwalen da akayi sai naje na wanke da sabulu hajiya tq dauko wani hijab tabani nasaka muka fita ita take jan motar................
 Muka tafi ina gidan gaba muna tafiya tana nuna min gurare da dama abuja lalle garin ya haduwa iyaka haduwa mukaje kasuwa takaini wani shago tace raliya na naam Maaamah  tace wani irin perfume kike using nace naam😳 tace au yi hakuri wani tulare kike amfani dashi nace au Bintu sudan😂 Hajiya  tace kasan mai kabani rexona sure, kawo soft &gentle naga tana ta hade haden tulare da mayuka masu tsada dakuma mayukan wanke gashi daga nan ta daukeni muka tafi exclusive saloon aka tsefe min kitso sannan aka wanke   gashi ni kaina saida naji sukuni akaina muka dawo dab da la'asar mu ka tarar da binta kuku tamana miyan agushi da tuwon semovita mukaja girki.

LALLE samun irin su Hajiya  Rukayya  acikin masu hannu da shuni sai an dace tare mukaci abinci sannan ta ci ro kayayyakin da muka saya ta nuna min yanda ake anfani dasu sannan ta nuna
Min wasu riguna da siket masu kyau na sakawa sanan mukaje dakina ta nuna min wani drower inda xan tara kayana kai rayuwar birni da dadi
 Yau satina daya da zuwa kuma yau ne su kamall zasu dawo,haka balkisu ma yau aka kaini interview a sec school nayi sa'an samun aji buyu js2, sanan ustas kabir yana zuwa yi mana karatun QUR'AN da wasu littattafai na arabic kamar USULUS SALASA,KHULASATUL QAUL,DA TAHZIF lalle acikin dan satin nan na karu sosai Hajiya  kuwa abin na mata dadi sai dai wasu lokuta xanga hajiya na kuka shine binta take gaya min cewa rashin yaya sabeer ne yasa hajiya wani matsanai cin hali kuma mummy  bata da rikon addini sune manyan matsalolin hajiya
 Rannan danaji sai da nayi hawaye,balkisu tariga su Kamall isowa gari anan mukaje muka taro ta mukazo gida kai balkisu akwai  fara'a ga son mutane lalle akwai waye wa  atattare hajiya ta kwallami kira nazo da gudu nace  naam tace gashi waya nakarba nace assalamu alaikum yace raliya nace naam ina yini yace lafiya kalau  nace bangane waye ba yace audu na indo ne wani farin ciki ya cikani nace yaya audu,yace naam ina indo da mutan garin mu lafiyansu kalau ga indo ku gaisa ta karba tace aminya nace yer uwa muka gaisa sosai nace ina kaima haka tace gashinan kullum muna tare don ALLAH ki gaida min shi aaa raliya ko kema so ne yakamaki mukayi dariya sanan tace anjima zan hadaki da su ummq nace nagode agaida mutan garimmu tace to
 Nabawa hajiya wayar ina ta murna tace yau anji muryan indo nace eh Maaamah tace ki kiramin balkisu nace ta shiga wanka
 
 Acan kuwa bangaren fiddy tana zaune gaban mirrow ta zabga tagumi ga waya a hannunta yana ta runging amman bata san ma yana yi ba,tun suhailat na wanka tanajin amon wayarta hartafito ita a zaton ta ma fiddy bata nan sai tazo tace fiddy, fiddy, fiddy shru fiddausy sai ta firgita tace naam suhailat,Hava hava firdausi u have to change yakamata kisan cewa ke babbar yarinya  ce kisan cewa kina da class ga ilmi ga wayewa ga arziki havaaa mana fiddy amman kin tsaya kina wahalar da kanki akan wani bagidaje dan kau.... DAKATA suhailah kai karshen magananki batare da kin kushe min masoyi ba inajinki,hmm ok fiddy amman yakamata ki rabu da kwallon mangoro kihuta da kuda kiga yanda yaran man da manya mutane ke bibiyarki Hoozaif  ma yace na masa hanya,ga abubakar na  kano ga senator suleman Abba gee,ga prof. Ibrahim ina kika barsu duk ko yanxu kikace su fito zasu fito maganan aure amman kin baro iyayenki kinzo kin zauna domin mutumin dayake gudunki hava yer uwa, kawai sai ta fashe da kuka da kyar suhaila ta lallabeta(ki rana ga yan mata mudaina daura wa kanmu wahala na dakon son maso wani) tace suhailat wallahi inason Abdoul  son danake masa zai iya illatamin rayuwa domin nasan lalle idan har ban auri Audu   ba toh lalle zan mutu ba tare da nayi aure ba,karki fadi haka sister sai suka rungumi juna suna ta kuka...........

Acan kuwa nafada an tura tambayar auren audu da indo sai da ya tabbatar an bashi sannan yafara shirin komawa
Sun je bayan gari suka kira raliya domin sanar da ita,nayi murna sosai najin wannan labarin,natambayesu ina su ummah da mutanen gari tace suna nan kalau nace ina kaima haka sai indo tace tun tafiyarki ya rage magana sai dai yaxauna yayi ta kuka😭 sai naji abin yayi mugun tada min hankali amman saina basar,
Ummah laddo kuwa tasha alwashin baza ayi auren indo da Audu  ba, sai dai ko bayan ranta

Rayuwata a abuja yamin dadi amman kalubalen dana ke fuskanta agurin kamall yana hantara na karshe ma villager yake kira sai dai abin bai dameni ba tunda duk gidan sun san halinsa kuma ina tuna Maaamah tana yawan  bani hakuri akan halin danake ciki sannan tace na ringa kau da kai ALHAMDLILLAH.....
sai dai kullum tinana kaima haka ban gane tausayinsa nakeyi ba ko kuma sonshi nake ba
 Ranan wata alhamis balkisu na kwance akan gado nashigo naga duk hankalinta yana kan system sai na zauna a bakin gado  nace Sistr  what are u busy doing, sai ta juya fuskanta cike da fara'a tace woow sister real (sunan datake kirana da shi kenan) turanci ya kankama fa sai nace yea Sistr sai tace gaskiya u r real sqi naji tayi shru tana ta danne dannen laptop sai nace sis assignment kike yi ne tace aaa wallahi wani hausa novel nasamu sai nace au daman har hausa ma ana samuwa apart from eng novel sai tace eh akwai a blog na BENAZIR OMAR, sai nace meye sunan novel din sai tace KAZAMTATCIYAR SO nace toh sai ku bari naje garden  nayi revision,sai tace ok bari nima xan sameki in nayi wanka nace toh nazo xan fita muka ci karo da Kamall  da faisal sun dawo nace sannunku da zuwa yaya Kamall  sai kawai ya toshe hancinsa yamin tsaki ya wuce sai faisal yace yawwa real ya gajiya Maaamah  tana nan nace aa ta tafi gidan Anty  rabi yace ok,kefa ina zuwa nace garden yace ok sai munxo nace toh natafi ina zaune sai hawaye ke kwalala a idanuna na goge sannan na tuna Uztaz kabir yace(WALLAZINA IZA ASABAT HUM MUSIBATIN QALU INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN)ina ta mai maitawa sai naji zuciyata tayi sanyi sai nafara revision sann na hango bilkisu na zuwa tasa wani riga dai dai gwiwarta ma ruwan brown da wani wando mai ruwan kwai yellow tayi rolling da yellow mayafi a binka da fara kunga yanda tayi kyau ta iso nace wooow Sis kinga yanda kika yi kyau kuwa sai tayi murmushi taja kujera ta zauna kusa dani tace real naji ku keda kamall dazu sai dai kina hakuri kinji nace toh bakomai sai tace bayan magrib ina so ki koya min USULUS SALASA nan cux sai nace to sis,sai tace kibani labarin samarinki na kauye sai nayi dariya nace kinga ni bani da saurayi sai dai na bata labarin indo da Audu  sai kuma kaima haka sann na ke bata labarin garba yayana tayi ta dariya sai nace kefa sis baki da saurayi sai  tace akwai  bakisan Kamall  yana mutuwan sona ba? Sai dai ni bana sonshi kodan miskilancinsa....

Tab Sistr  ashe yaya kamall har xai iya cewa yanason mace?hmm real kamar kinsani kuwa bai taba gaya min ba amman yasamu Maaamah  yagaya mata nikuma yanayinsa yasa naganesa  amman ina basarwa kamar bansan meyakeyi ba yasha nuna min amman sai kaucewa nakeyi sai nace tabdijam zanso naga auren ku,sai bilkisu tace hadin gambiza kenan gabadaya muka kwashe da daria sai faisal yazoo toh toh me akasamu ake rabawa  ba asa dani ba sai  balkisu tace hiran kauye to nima abani nasha sai ya juyo da kallonsa gareni sai yace kodai labarin kaima haka ake baki😳 gabadaya na rikice  bnsan waya gayawa faisal ba sai yace ya yanayinki ya chanja?? Hmmm kinsan ina nasan lbrynsa a hanzarce nace aaa sai yace ranan nazo wucewa ta kofar dakinku naji kina mafarki kina ta surutai anan naji kin ammabato sunan sai kawai abin yabni mamaki kaina ya dau charji sai balkisu tace aaa faisal meye kake bibiyar mu har da dare kana zuwa side na dakin mu sai nagaya wa Maaamah  awww hava Sistr  balki  wallahi wasa nake mata ranan naji tana hiransa wa binta ne kuma nasan kema tamiki sannn ranan naji tana tambayar kawarta ina yake bayan tagama harda ajiyan zuci wai ALLAH ya baka lafiya masoyina sai ya min gwaliyo na dauki pen na hannuna nakai mar duka sai ya gauce suna ta min daria

Sallamar yaya Kamall  ya katsar mana da daria sai kowa ya natsu amman banda sistr tana ta dariya sai, sai yace balkisu sai tace yane sai ya sosa keya amm daman inaso mudan fita ne kafin Maaamah  tadawo sai tace kafiye son yawo ba inda zani sai Maaamah  tadawo sai yace hava dear bilkisu ya matso kusa da kujeran ya durkusa niko a raina sai mamaki nace ashe daman Kamall  zai iya biyayya tabdi so kenan sai faisal yace kina mamaki ne a hankali nace sosai,sai muryan Kamall  muka jiyo a sama mekuke tseguntawa magulmata sai faisal yace yawwa to kinji yanda GLOBAL WARMING din yake sai yaya kamall yace dakai nakeyi mekake fada mata sai nace lesson nake mata, sai yace keh villager tashi kibarnan ina tashiwa bilkisu tace zauna meyasa xaka koreta while dukan mu anan muka sameta ba inda zata sai ko yayi shru saitace real tashi mutafi natashi takamo hannu na mukatafi dakin mu sai tace karki damu kinji real nace to ba komai nagode Sistr..
Kishirya zamu fita anjima bayan isha sai nace aaa sis bazan biku ba wallahi ina tsoron yaya kamal ni
Nace kishirya xamuje ma kigaida mama na nace to amman kigayawa Maaamah  tace bakomai sai muka nufi kitchen don daura avinci dare tare da binta kuku.........

Maaamah  ta dawo muka gayamata tace muje mun shirya mun fito ina zuwa dai-dai motan yaya Kamall  ya min tsawa kekuma ina xuwa sai balkisu tace tare da ita zamuje koda magana sai yace impossible balki kina sa yer aiki ta raina ni karki manta level namu  ba daya  bane,tana yunkuri magana muka jiyo murya yana cewa tabbas level naku ba daya bane amman karka manta agurin ALLAH Duka dayane wata kila ma tafika tunda ita bata wulakanta dan adam  wanda haka is prohibited in islam hava yaya Kamall  kana tuno nasihohin da mahaifiyar mu tamana mana kawai sai ya fashe da kuka najuya xan koma ya kama bakin mayafina real kiyafe wa dan uwana najuya idonsa yayi jajur nima kukan nake nace nayafe masa harga ALLAH sai yaya Kamall  yace kiyi hakuri nace yawuce sai nace ni zan koma kutafi kawai shsh dat means baki yafe ba nace wallahi nayi to kizo ku tafi sai yaya Kamall  yace faisal kaima kuzo mutafi duka sai yanzu naga bilkisu tayi fara a...
Munyi yawo sosai a gari don sai gurin sha daya  muka dawo munje gurin haj saratu mamar balkisu naga kanneta gidansu fara'a muka gama muka dawo gida balkisu tamana shoppng sosai nasu man shafawa da chocolate yaya Kamall  ya biya mana faisal yasaya mun wasu top masu kyau da tsada....

Yau akabamu hutun third term na aji uku jss 3 kamar yanda nasaba ina zumudin komawa nafada kuma hajiya tayi min alkawarin sayamin waya, sai bello driver yadauko ni sai mukataho tare da hasina yer hajiya rabi friend na maamaah muna isowa gida naji ana ta girke-girke sai nace mummy wani bako ko bakuwa zamuyi sai tace yau mummy zata dawo ita da yer kanwata, naji dadi sosai  sai maamaah tace ya gobe akwai zuwa nafada gobe kenan nace aa maamah sai najira xuwan mummy ga hasina ma zata kwan biyu anan eh hajiya rabi ta gayamin taje kano nadin sarauta ko eh to kuje kuyi wanka ku chanja kayanku

Misalin karfen uku na yammaci yaya kamall da balkisu a mota daya nida hasina da binta kuku a motan bello driver sannan mommy ita daya a motar mukayi jerin gwanon taro mummy a airport muka je muka dauko ta, kai mummy  ta hadu  iya haduwa sai dai daga ganinta akwai mugun hali a tattare da ita don yanda take hada rai ita kadai tashan kamshi tawani basarwa.......
Munzo tayi wanka takwanta daganan sukaje kan darning da kawarta danaji ana kiranta baturiya suka ci suka koshi nikam na doshi gurin binta kuku muna hiran duniya, anan take tsegunta min mummy bata da kula da addini sannan tanason mulki kusan halinsu daya da yaya kamall nace nikam inasatq a addua tun kafin naganta cuxx tana birgeni anan hajiya ta aiko akakirani
Naje tace ga waya ankiraki sai nace toh anan indo take sanar dani shekaran jiya audu yadawo kuma ansaka ranan aurensu da audu nan da sati uku nayi murna sosai sai nace ya magann saddiqa fa sai tace kawalli sai abinda yakaru nace karki damu ALLAH yana tare damu ki yi addua wallahi addua ne kadai mafita kuma maganin kowace damuwa don haka zan ma yayana text na wasu adduo i kina yi kinji anan ta roki alfarman inzanxo nasaya mata waya nace bakomai ina gamawa na mika wa hajiya sa mummy tace wannan waye ne? Sai maaamaah tace wannan ne raliya ta nafada ok itace real da faisal ke gayamin ko nace sannunki nace yawwa mummy good u can go nace thank u sister

Dasuka gama hira tatafi dakinta sai nasamu maamaah a falo nace  mamah tace naam real sai nayi dariya nace maamaah harda ke tace eh nace mama auren indo yazoo tace yaushe nace nan da sati biyu toh yanxu yaushe kikeso kiji nafada nace maamah duk yanda kika tsara sai yace ok bari ran monday sai kitafi kinga ranan haj rabi zata dawo kinga hasina naga tafi sakewa dake toh maamah nagode ALLAH yabarmana ke tace amin na koma dakinmu nasamu hasina da balkisu suna hira inazuwa sukace kizo ki kara mana karatu mukazo mukayi ta karatun AL QUR'ANI MAI GIRMA sai can muka kwanta bacci

Ranan asabar mukatashi asuba kamar yanda muka saba mukayi sallah muka ma karatun AL QUR'ANI  sai da rana yafito muke shirin komawa bacci mukaje misalin tara da rabi natashi nayi wanka nafito sannan naga mummy da kawarta sun tashi sallan asuba abin ya mugun bakantamin rai yayi ba sukayi sallah sanan suka sake koma wa bacci sai maamaah tafito tace kije   ki tashi mumny tayi sallah kuwa nace eh yanxu sukayi sai hajiya taje kofan dakin ta magana naji tamata TSAWA (kai yan uwana abar raina iyaye)sai hajiya tadawo tazauna a falo tafara kuka nazo na kama kafafunta nace mumny kiyi hakuri karki zubar da hawayen ki kijawo mata masifa ashe lokacin tana labe tana jina maamah addua kawai zaki mata domin adduar ki yafi na kowa agunta sai tace, tunanina da sabeer yana nann bazai taba yarda ba sabeer ko idona baya gani in ina mar magana tsabagen tarbiyya INSHA ALLAH SABEER dan aljannah ne duk nima naji jikina yayi sanyi sai mummy tafito maamah meyene babu kikoma ki kwanta zata juya nace anty kizo ki bata hakuri plxxx kodan ki samu rabauta sai tamin tsaki ta shige

 Dayamma ina garden da hasina da yaya faisal da balkisu muna ta hira sai turai da mumny ma sukazo, ana ta hira da nishadi sai mummy tace real nace naam anty inaso natambayeki ina ji anty sai tace jiya naji kina gayawa kawarki cewa zaki tura mata addua nima ina bukatar adduoi domin ina cikin matsala babba sai turai tace babba kuwa sai nayi shuru sai tace real kitaimaka min bani da mafita sai naceanty  kina dashi keko kike da mafita............

Yawwa real gayamin sai na mike, anty inaso kigayamin yaya sabeer a rayuwarsa meya nema ya rasa dukda bansanshi ba?? Babu real ok shin kinsan dalilin hakan aaa sai balkisu tace biyayya wa iyaye musamman mahaifiya sisi(sunan da balki ke kiranta dashi) tabbas zamana da real na karu ga nisohin da ustas kabir yake mana nasan da zaki jure ki halartar dazakiji dadi,lalle anty zakiji dadi sosai sanan yau sallan da kikayi da asuba walaha ce wannan ba asuba ba nima bani dasani kamar ustas amman kidaure kina zuwa idan yazo na tabbata zamu rabauta sai ta fashe da kuka sai faisal yace sis yanxu haka kije kinemi yafiyar hajiya sai balkisu tacr tabbas domin kinsamata madaci a zuciya tunda jimawa

Sai lokacin hasina tasa baki sister gaskiya suke fada miki domin mummy nah tabani labarin wani dan uwanta yayanta ne ma uwa daya uba daya,abin daya faru dashi sakamakon rashin bin umarnin mahaifiyarsu sai lokacin baturiya ta cire tabarun idanunta tace hasina kibamu labarin meya faru dashi,ita ko mummy idanunta fal cike da hawaye sai hasina tace kamar yanda kuka sani mummy na hajiya rabi yer sarautace

Alhaji sani muhd salim (SMS) shine mahaifinsu yana da mata uku da kwar-kwara biyar, Alhaji sani muhd salim wanda ake mar lakabi da INUWAN TALAKAWA, wasu kan kiransa da INUWA SMS yana da jazama sai dai bashi da rabon 'ya'ya masu yawa a duniya kamar yanda shima gadon sarautan yayi agun mahaifinsa dayake shi kadai ne yaro agunsa,  sarki yayi wajen shekara 4 a sarauta bashi da dansa na kansa hakan yayi mummunan daga mai hankali domin bashi da magaji....KWATSAM watarana ya je katsina gun sarkin KT Babangida maji dadi,  ziyara sai aka bashi kanwar sarkin katsina hajiya salma ya aura..........
Aurensu da wata uku tasamu ciki ta haifi namiji aka samai salimu, sanan mahaifiyata hajiya rabi
Sun taso cikin jindadi  da kulawa na mahaifinsu hakan yana matukar konawa wa hajiya kumbo rai uwar gidan alhaji inuwa sai da suka gama karatunsu,haj salma tayi musu tarbiyya mai kyau sai dai salimu yan gidansu na zugashi akan yarima mai jiran gado hakan yasa yake abinda yaga dama,bayan yagama service nasa lokaçin kuma mummy na tagama secondary school nata ta jona dev....................sanan aka tada maganan auren su shi salimu ya auri yarinyar yayan haj salma,yayan mahaifiyarsa kenan zeenart tare sukayi service suna son juna sosai sun haifi yaro na fari,akasa mai sunan sarki sai kuma bata kara haihuwa ba sai ita kuma mummy na ta auri daddy na lokacin yana aiki a court of appeal na kano .......
hajiya kumbo takawo yer kanwarta mai suna khairat akan ta zauna agabanta toh yarinyar yer duniya ce , dayake salimu agidansu yake da zama
Sai salimu yana kulata anan mahaifiyarsa tamai fada amman yaki ji akwai randa ya budi baki ma yace mata wai ko don ina auren yer yayanki ne kike mata kishi?? Hajiya salma taga bakin ciki gabadaya yaro ya susuce akan khairat ita kuma zeenert ALLAH yadaura mata son salimu bata ganin lafinsa anan khairat tayi ciki sanan akace salimu ne yamata............

Kutashi muyi sallah magrib tayi,inji balkisu sai mummy tace ok muhadu bayan isha sai nace akwai karatu uztaz kabir zaizo ok let us meet by  10 O'Clock ok sai duk suka nufi gida

Ranan faisal gabadya jikinsa   yayi sanyi gurinsa yaji karshen labarin aikuwa haka akayi misalin goma na dare hajiya tashiga ta kwanta muko munzo falo muna kallo sai faisal ya shigo yana isowa yakashe tv yace hasina tace naam wayayi wa khairat ciki karde kice min salimu ne??? Tabbass shiya mata shiya mata ciki ya amsa hakan agaban mahaifinsa abu kamar wasa ta haife dan wallahi dazaku ga dan zakuce bai hada zuria damu ba,hajiya salma tanaji tana gani kumbo ta kwace zuciyar dan ta ita zeenart tazama tamkar hoto karshe ita take raino haidar yaron khairat sanan haj kumbo tafito da zancen auren khairat da salimu,,,,
ALLAH yasa ba ayi ba inji ni hmm real kenan anyi ai amman bada son ran hajiya ba.... bayan aurensu da wata biyu tace zataje ganin gida a Adamawa daman ita yer gire ce,ta shirya akamata goma na arziki sai ta tafi tabar haidar agun yer raino wato zeenart taje wajen wata uku bata dawo ba sai gabadaya salimu yahaukace haka ma zeenart nashiga uku yer uwa bata nan anan kuwa suka shirya binta Adamawa, sai da haj tahana su, amman sun kiya toh gashi tafiyar da basu dawo ba har yanxu gabadaya suna ta sallati da jimami balkisu harda kuka, sai nace hasina ina mai sunan sarki fa ai shine yanzu mummy na ta tafi nadin sarautansa yana yaro aka bashi sarauta sai faisal yace karde sarki ya rasu aaa be rasu ba inji hasina yayi murabus ne mummy kam takasa cewa komai sai kuka sai baturiya tace to ina haidar?  yana gurin kumbo nace  tabdi,  to kunji lbryn khairat?
 Kwarai kuwa yanzu haka tana chan agaban kumbo amman salimu da matarsa har yau ba labarinsu, amman anfi dangantawa da rasuwa sukayi domin anyi neman duniya ba agansu ba, sai balkisu tace a motar ksuwa ne konasu, aa motan gida ne su biyu kawai, tagoge hawayen daya gangaro mata tace haryau mummy na na jimamin batqn dan uwanta....

Shine sister komai zamuyi .. kar mu bata wa iyayen mu musamman mahaifiya
Daga kan da zamuyi muka ga karfe 12:15 sai mukace bari kowa yaje ya kwanta kar mu makara asuba , kowa yatafi makwancinsa
Karfe4:30 nasafiyar lahadi mummy ne tabi ta tayar damu sallan asubahi abin yabama maamaah mamaki sosai har su faisal ta tayar

Wajen 9:30 Bayan munyi breakfast sai mummy tace naji ance gobe zaki koma  nafada real eh anty amman kizauna muyi hutun mu mana anan kinga ko ai yafi dadi inji baturiya sai nace aa akwai bikin aminiyata indo ne shiya sa
Indo! Inji mummy sai nace eh ko kinsanta ne sai tace aaaa meye sunan mijin nata Audu ok amman yaushene bikin sai nace nanda sati biyu ne ok kibari jibi sai kitafi kinji nace ok bakomai anty

Misalin karfe 12 na rana muna ta hira a falo sai maamaah tace real kishirya keda hasina mufita muka shiga mukasa after dress a kan kayan mu da man top da skirts ne muka tafi hajiya tanufi kasuwa dani tasayamin waya tayimun cefane sannan tabani turmin zani guda hudu gudun mawatar wa Audu, ta saya wa ummah da abba ma waya rakani toilet,tamin goma na arziki
 Ashe bayan fitanmu faisal yazo da wani gift anyi rapping yatarar da yaya kamall ma ya dawo sai suna tambayarsa meye wanan sai yace special gift wa real mana sai mummy tace faisal anya kai dinnan baka fada bankuwa sai suka kwashe da dariya sai kamall yace aiko dana babballashi wallahi mezaiyi da kucaka wallahi raliya munafukace aaaaa aaa karka soma inji balkisu munafurcin me ta maka kawai don ka tsaneta aa wallahi bazaku taba ganewa bane sai balkisu tace muddin zaka cigaba da cin zarafinta wallahi b
ani bakai sai yayi shru

Sai gamu mun iso gida da kayaniki niki su ka karbe mukazo nace sutayani yi wa maamaah godiya kamall kamar ya mutu sai yaciro wayarsa yane aboki kana nan ok on my way yafita yatafi  da daddare misalin 9:15 sai faisal yazo yace real daura indomie mana sai natashi nashiga kitchen na daura ruwa kawai juyawan dazanyi naga faisal yace real sannu da kokari nace yawwa sai yace intayaki nace aa sai yace real gobe zaki koma ko sai nace aa anty tace nabari sai jibi ok to me kike bukata agurina, sai nace babu faisal sai yace aa kituna sai nace idan akwai kayanka dasuka tsufa kabani zanje nakai wa kaima haka domin wannan karon innaje zanyi kokarin dawo dashi gidanmu ok kinsamu bayan wannan fa nace babu ok inajiran indomie a falo nace ok bros sai hasina ta shigo kai kai kai ana soyayya a kitchen sai ya harareta sai tace afuwan sai nace kefa baki da head ta ina zan fara soyayya da yaya faisal sai tace aaa baki san inda rana zata fadi ba sai nace YAMMA sai muka kwashe da dariya..,.....
Shima yaya Faisal din dariya yayi yatafi yace kai hasina bakya rabuwa da barkwanci,nakaimai indomie mukayi ta hira  sai mummy tace gobe yakamata muhada get together a millionaire park, sai baturiya tace gobe ne senator suleman abba gee zaizo shine zakuje ku gaisa wooo inji faisal gobe za a mana ruwan naira kenan sosai inji baturiya,sai mummy tace nifa natsanesa kawai ya matsa min xaizo ne ok agaya wa kamall ma plxx mushirya.........

Ran monday dasafe hajiya rabi ta bugo waya tace agaya wa hasina Aliyu zaizo daukanta su koma gida kafin na iso don ina hanya tab kinga kuwa yanda ranta ya baci sai mumny tadau wayanta takira haj rabi tace hello mummy naam hu is on d line, firdausi ne, ok yakuke ya makaranta ai nadawo mummy ok ya akayine, aa mummy alfarma nake nema agunki don ALLAH ok nameye kenan yau akwai wani dan party da zamuyi after asr prayer kibar hasina i promise to take her home, party kuma  firdausi nameye  to mummy get together na ne haka mu yan gida ne kawai,dawa dawa, da faisal,kamall,ni,baturiya,hasina,balkisu,sai raliya da binta kuku,ok waye kuma baturiya ok suhailat yer baba jidda mana oh itama tazo kenan kwarai kuwa, ok sai na ganku yawwa mummy mungode INSHA ALLAH agida yau xamuzo magrib ayi abinci daku kenan,aaa mummy ALLAH yakawo mana ku lafiya amin  Firdausi bye -bye,takecare tana katsewa hasina dadi kamar tayi yaya,sai Faisal yace bari na kira yaya ALIYU nace yazoo, wayyo kayi hakuri don ALLAH(wayyo kayi hakuri don ALLAH) sai ya kwaikwayi magananta duk sai suka fashe da dariya.

Bayan la asar duk sunci kwalliya sun tafi millionaire park sun zazzaga sukazo suka taru agurin wasu kujeru sai lokaci senator yakira akan ysna cikin MP tagaya mai inda take  can sai gashi ya iso da masu tsaro mutum biyu kai senator yahadu dan matashi ne mai fara a shine ta gabatar damu agabansa gabadayan mu yabamu 20 20  thousand suka koma gefe suna tattaunawa mukosai hira muke can sai tace tana zuwa basufi minty 10 mai lafiya ba sai gata da drinks ice cream burger shawarma,spring roll,meet pie, kai tazo taxuba mana muka fara ci muna ta nishadi, sai faisal yadauko wannan gift din yabani yace kina tunani da wannan real kamall sai ya bata rai sai hasina tace soyayya lubiya tambarin zinaria,sai yace aa real yer uwatane sai kamall yace mai gadon(,balkisu kenan) saitace yane sai yace kizo kiji sai suka matsa gefe sai hasina tace abude mugani sai faisal yace karki bude sai kinkoma nafada...

Misalin karfe shida muka nufi gidan anty rabi anty rabi taji dadin ganin mu,dataganni sai tace ina mata kama dawata amman ta manta wayee anan mukayi magriba nayi sallama da hasina tabani hotonta muka koma gida,
Bayan isha sai ustas yazo anan nake gayamai gobe zanje nafada,sai yace nabashi number na,nace bani da sim but kabani naka xan nemeka ustas yabani muka watse bayan fatiha ina dakina ina shirya kayana sai faisal yashigo ransa abace, sai nace lafiya yaya faisal sai yace meyasa kika karbi numbern ustas,laifine faisa inji balkisu sai yace babba ma kuwa baisan an mata miji ba.........

Miji kuma yaya faisal ni wayamin miji yaushe akuma ina??? Sai yayi murmushi yace yaushe kika zama yer jarida,kuma wanne zan amsa miki daga ciki,sai nace duka sai yace
Ke kika ma kanki miji,a nafada,sunan sa KAIMA HAKA sai suka kwashe da dariya dukansu sai ya fita shima yana dariya sai nace yayay faisal baka rabuwa da abin dariya......sai sister tace anya faisal bai fada kogin sonki ba sai nace ai ko koramar sona yafada zai fita  because bana love.......sai mukayi dariya sai hajiya ta aiko aka kirani har dakinta tadauki dubu goma tabani nace maamaah kiyi wa ALLAH kibari wallahi ina da kudi har dubu ishrin wanda  senator yabamu sai tace wannan kuma haqqinki ne sai kama kuka ina rokonta tabari amman taki sai nakira su mummy susa baki but suma da sukazo sukace na amsa sai na amsa na koma daki,sai nake gayawa sister nace maamaah tana wahala dani......

Ranan talata da safe muka fito da kayana bello driver ne  zai maidani gida nayi sallama da kowa amman banga yaya kamall ba don haka nace ace mar natafi ya yafe min nai ta kuka tundaga gidan ban daina zub da hawaye ba sai da muka iso bauchi tun bello na bani hakuri har ya rabu dani mun isa gida misalin karfe biyar dai dai naje gida ina ta farinciki sanan bello yace shi zai kwana a gidan mai gari zai kaimar sakon hajiya wai bakin indo kamar zai yage kowa farinciki nadawo natarar da labari mai dadi yaya garba ya kammala karatunsa yasamu aiki a kano anan umma take cemar dayanemi mata yayi aure munyi farin ciki sosai ranan gajiya na kwanta nayi bacci da sassafe naje gidan maigari nakaima  bello abin karya kumallo sanan nace karyatafi fa yajirani xan kawo mai sako
Naje nahada kindirmu da manshanu  da kuka na miya da daddawan miyan sanan nahada goruba da aduwa wannan nasu mummy sanan na debo rogo a gonan baba na hada musu sanan baba yabama bello dubu biyar yaji dadi sanan yakama hanya niko nadawo gida muka zauna muna ta hira ga indo ma tazo mana sai nace indo ina audu hajiya tabani sako sai muka fita da zummar zuwa gidansu kawai muka gansu da yaya garba suna hira anan nabasa sakon sai yace bari na ma nakirsta namata godiya sai na dawo gida naga abba da sabon waya nace abba wayasaya maka waya yace yayanki naji dadi sosai sai yanxu na tuna  gift din da faisal yabani sai na nufi dakina nabude akwatina    naciro nabude sai naga set na tulare dakuma wani kwali sai na dago naga samsung Galaxy S5 wai wai wai sai na bude wayar naga karamin takarda yafado daga ciki....

Zuciyana  yayi bala'in tsinkewa nadauko nabude na warware naga sako kamar haka (Real namiki charge na wayan sanan akwai simcard akai ga numbern ki 0703320...... Na miki saving na number mutanen gida baki daya sannan akwai katin five thousand aciki kikula da kanki sosai daga dan uwa kuma........... Faisal)  Murna ya cikani naje na nuna wa umma yaya garba yashigo mukayi ta farin ciki, nace indo ina kaima haka  sai indo tace muje nakaiki gurinsa nace ba komai muka kama hanya naje nasamesa a kasar wata bishiya nazauna kusa dashi nace kaima haka sai kuka ba magana,nima na fashe da kuka ga matashi kyakkyawa amman ba hankali ALLAH mai iko sai indo takama ni mutafi gida muna hanya nace indo ina labarin saddiqah, tace hmm saddiqah hauka ne kawai yaragesu ita uwarta meya faru ke har niger sukaje gurin kawun audu wai yahana auren mu amman duk anki goya musu baya sai nace,kawalli inaso muyi wani shawara dake idan bazaki damu ba sai indo tace xo mu zauna anan bani labari, sai nace inaso nasa malamai ama kaima haka addua ko zai samu sauki kaii inji indo raliya ki kiysyeni kinsan tsintacciyar mage bata mage fa, kuma wallahi duk wanda yabi bado sai ruwa yajashi aa indo kifadi alheri ko kiyi shuru sai tace toh yanxu mu tunkari audu da maganan nan tukunnan shi sai ya gayawa wa yaya garba koya kikace???eh gaskiya kin kawo shawara sai wsyana yafara ringing na dauka muka gaisa yace faisal ne nace yayana kayi hakuri nahada waya bankira na maka godiya ba sai yace bakomai ai muna missing nski fa nace nima ina missing naku yan uwa mukayi sallama ya kashe

Sai na zauna na ciro wayana ina ta kiraye kirayen mutanen gida muka gaggaisa, sai muka nufi gida sai indo tace ni wayar tawa sai nace muje gida naje na ciro wayan da hajiya tabani na bata sai nadauko na abba da umma kuma na bawa baba zuwaira da umma sanan da muka shiga nama umma bayanin abin dayafaru akan waya sai yaya garba yace shi idan yafita gobe zai saya musu simcard indo mahaka murna yacikata

Ranan juma a dasafe mun gama tsara inda za a ajiye KAIMA HAKA  a gidan mu domin iyayena sun bani goyon baya dari bisa dari sanan malama na garin mu wasu kuma daga ashaka da na niger yan uwan audu dasukazo aure suka hadu aka msi saukan AL QUR'ANI mai girma cikin ikon ALLAH ya kwanta bacci bai tashi  har dare  mukayi yanka àkayi sadaka  sai ran asabar ya farfado cikin ikon ALLAH yasamu lafiya amman baisan komai ba don haka nayi tunanin kaishi asibiti a gombe mukaje da abba da yaya garba da audu aka aa auna shi anan suke gaya mana ysyi loosing memory nasa amman zai iya dawowa normal idan har sanadiyar haukansa yafaru agabansa
 Muka dawo nqfada abinmu munsamu yaro agidan mu nabasa kayayyakin da faisal yabani na kawo mar yana canjawa dasu,
Satin faruwan hakan bikin indo da audu mun sha kalangu kam harda na banza umma tasa wa kaima haka suna muhammad shikuma a tunaninsa ni kanwarsace...........
Mun raka amarya sai da na mata kwana uku agidan sannan na koma gidan mu ranan muna ta hira indo tamin waya wai naje.....
Naje naga kawata tayi fresh ta chanja sai tace kawalli kinemi miji kiyi aure wallahi yafi miki karatun nan dakike yi nace aaa nikam inaaa mexai kaini anan tabani wasu labaren su na aure (amman baxakuji abakina ba) nayi sati uku maamah ta aiko bello yaxo ya maidani  nayi kukan rabuwa da Muhammad,yaya kuma masoyina domin yanzu na fahimci ALLAH ya daura min jarabar sonsa,shikuma yana ganin ni kanwarsa ne naje nama indo sallama kullum Audu baya fita nsje ina tsokananta saiyaya garba ma yace zai bimu ya sauka a bauchi yahau motar kano haka kuwa akayi na iso abuja agajiye nazo nasamu su mummy suna shirin komawa nijar naji haushi sosai .......,...............
Mun dawo mukadai domin su balkisu ma ta koma sai kuma yaya kamall abinshi sai gaba yake dada yi faisal ya koma Ukraine sai waya ne yake hadamu...
Gidan yazame mun atakure wallahi sai dai wataran hajiya rabi tana cewa naje mu kwana da hasina ko ta turo mana ita watarana mu kwana cux haj rabi tana sona.......................

 A kwana atashi yau wata tara da bikin indo haihuwa yau ko gobe, niko nagama ss1 nawa nadawo gida hutu anan na natarar indo ankaita haihuwa a asibitin gombe nayi murna sosai aka dawo da ita tazo da yaro namiji ranan sunan muna kan aiki sai yaya garba yadawo.......

Akarada wa yaron suna Ahmad liman baffan su audu mai rasuwa hakan yayi wa kowa dadi sosai oh su indo da yaro,tayi kyau kamar ba ita ba
Yaya garba yazo akan aje amar tambayan aurensa su abba sukaje aka basu akasaka date nan da wata hudu, nayi murna sosai jameela yarinya kyakkyawa gaskiya yayana yayi sa ar mace hutu ya kare na koma abj wanan karon ma ba wanda yaxo gida abin haushi sai binta ne kawar hirana.......

Watarana binta ta tafi suleja daman ita yer chan ne taje tayi kwana biyu aka barmu da maamaah agida sai mama ta shirya fita zuwa asibiti dubia sai tace naxauna agida ina xaune muna chatting da yaya garba yana hada kayan aure sannan ya tutturamin wasu sai kuma faisal ina tambayar yaushe zai dawo sai su mummy karshe ma group chat na gida suka hada suna ta tsokanana sai naji sallamar yaya kamall na fito ina ganinsa gabana ya fadi nace ina yini jikina na bari yace lafiya ina maamaah nace baaa baabbata nan  sai yace kedawaye nace bakowa ok koma daki natashi ina karkarwa ina shiga daki na tura nasa key nadawo ta window ina leken harabar gidan chan naga yafita yana ta dariya  banga motarsa ba ashe motar na can waje yadauka yatafi sanan nafito nadawo falo,sai maamaa tamin waya wai nadafa mana couscous da stew natashi nashiga kitchen amman gabadaya bana hayyacina sai maamaa tadawo tana ta sallama banji ba har tashigo nikuma dana ganta ban kula ba sai na firgita tace miyene nace babu maamaa ta masa nace wallahi bbu sai ta fita..........

Bayan kwana uku da faruwar hakan sai kamall ya shigo yana  bala i wai ya ajiye tulare set an dauke gashi mai tsada ne sai maamaa tace to wayake shiga dakinka kamall sai yace jiya naga raliya akofar dakina sai maamaa tace koda kaganta raliya bata sata sai dai wani abin daban sai yace in dagaskene taxo in tambayeta sai aka kirani nazo nace wallahi bani bace amman tabbas naje kofar dakinsa daukan tsintsiya, sai mummy tace ok nawa kasaya na biyaka yace 18k sai mama tace real dauko min CBH wani kit ne nasaka kudin gida shine suke kiransa CBH,Ntashi nashiga amman ban gansa ba sai nace maamaa ko kin canja masa wuri ne tace aa kara dubawa na duba bangani ba sai maaamaa hankalinta yatashi tace mukuma munema tare harda kamall din da binta kuku

Muka birkita dakin maamaa ka kaf bamu gani ba sai tace ko ta manta a dakin mummy ne sai taje ta duba babu sai binta tace maamaa aduba dakunan mu direct dakin binta kuku mukaje babu mukaje dakina ba key kuma a rufe sai maamaa tace meyasa na rufe nace wallahi bani bace sai kamall yace akwai extra bari na dauko yaxo ya bude aka dudduba ko ina...
Ana bude drawer nawa sai ga perfume ya fado 😭 sai maamaa ta firgita budan bakin kamall barauniya to ina kika ajiye CBH kuka kawai nakeyi bansan halin danake ciki ba sai binta tadaga katifan gadon kawai sai ga kit din kawai nafadi na suma...............

Farkawan da zanyi naga mummy akaina ina asibiti duk bakinajini nayi yunkurin tashi amman nakasa,sai tace real nace naam anty sai tace nasan bakiyi ba sharrin kamall ne kuma maamaa ma tafahimta  amman meyasa kika suma sai nace anty wallahi narikicene ok kiga inda kika ji wa kanki ciwo sorry sai dr yashigo yake tambayar mu ya jiki gobe zai sallameni can sai maamaa ta shigo da  abinci sanan tace nayi hakuri karnafada agida shine nace mummy yaushe kika zo daman ina gari munxo yin wani abu ne tare da yan mqkarantan mu gobe xamu koma....
Washe gari aka sallameni nakoma gida sai nake tambayan maamaa ansamu kudin duka suka ce eh sai maamaa tace kar kusake maganan nan agidan nan haka magana yawuce amman dana gayawa  Faisal ransa yayi masifar bacewa shidai fatansa kar nabar gidan nace ba inda xanje .....

Ranan muna xams sai nafito nazo wucewa naji ya kamall yana waya yana cewa wallahi sai na koreta agidan nan,nace ALLAH yafika a zuciyata na wuce........

 Ranan yaya garba nakirashi naji ya shirye shiryen biki yace ALHMDLH mukayi hira yake gayamun next week su Abba zasu kano daurin auren sa nace nikam bazan samu zuwa ba amman ana ba da hutu zan zo nayi masa hutu ahaka mukayi dashi

Ranan alhamis dasafe su Abba suka kama hanyar kano suka isa misalin karfe 12:50 akan ran jumma a bikin yaya,Ranan jumma'a da safe misalin tara na safe sukaje kofar gidan su jamila da zummar daurin aure sunyi mamakin isansu basuga kowa ba don haka suka shiga ciki don jin ya ake ciki...........
Suka tarar da mal tijjani a xaune da kaninsa suna ta huci sai suka gaisa sai yace bagana kamusu bayani sai kawai kaninsa yatashi yace kai hausawa ashe baku da asali kuke shirin hada zuria da kanuriyan asali toh wallahi kunyi kadan kuma kukaboye kanku ashe ku tsintetten mage to ku tattara kafin ranku yabaci xa a aiko muku da sadaqinku jikinsu yayi sanyi suka fita suka nufi gidan dasuka taru yanda kasan mutuwa akayi washegari su mal dauda da abba suka dawo gida jiki ba kwari sun rasa ya xasuyi...... ranan danaji labari wuni nayi kamar bani da lafiya  garba yadawo yasa abba da umma a gaba yana kuka suna kuka abba kagayamana kai dan inane abba katunaa abbbaaaa!!!!! Yana ta kuka sai yace abinda xan iya tunawa kawai ni dan wani mai mukami ne amman ban san a ina ba sai ummah tace eh kuma akwai khairat amman bansan waye ita ba.........
Takaici yama yaya yawa sai daga baya ya tunanin kiran jamila sai ta dauka wai garba kai wani irin mayene karabu dani ni ba tsarar ka bace ta zazzagesa ya kwanta rashin lafiya da kyar akasha kansaya farfado don haka mal dauda yadau tasalla yabama garba.....
Garba ya amince akasaka date hakan ba karamin dadi yamini ba ...


Nadawo gida hutu na tarar da bikin yayana mukasha biki muka watse yadau amaryar sa xuwa kano muma mukaje mukayi sati nida indo sanan muka dawo anan indo tafara min complain na audu akan baya kwana agida nsata muyi ta addua kawai shine mafita
Mun dawo nafada zama yayi  dadi tasalla da yayana dukkanmu muna sonta domin ta huce wa yayan mu haushinsa............

Kowa yaji dadin yanda rayuwa tasalla da garba yake guudana domin yasata a makaranta niko nagaya wa su ummah wanan karon innaje abuja bazan kara dawoo wa ba sai bayan Final exams nawa umma tace bari xan sanar da mahaifinki anan aka gayawa abba ya amince yace nasan a hannu nagari nasaki baxaki cutu ba don haka kawai ba komai raliya....

Bayan kwana biyu bello yazo maidani gida nasamu yaya muhd a daki yana xaune sai nace yayana yace naam nace xan koma makaranta sai yace sai yaushe nace nan da wata tara kaga yanxu mun gama hutun third term ss2 sai yace ALLAH ubangiji yabaki Sa'a kanwata nace toh sai natashi na nufi kofa sai yace kanwata najuyo naga idonshi cike da hawsye  yace kodamma bari na rakaki sai ummah ta kirani muka fito ya tsaya abakin motan mu yamana addua yakoma gefe yana hawaye bantabajin rai na yayi kuna ba irin ta yau muka tafi anman jikina ba kwari

Ina isa abj na tarar yaya faisal yadawo yana ma jiran mu a bakin gate yana ganina  yataso oyoyo sis sai yaganni wata iri kawai yafara tambaye tambaye meyasameni nace masa babu gajiyan hanya ne sanan ya rabu dani nashiga ciki gabadaya kayana shi yakaimin ciki munsamu maamaah tafita yaje harda shirya min a drower yazoo real nayi missing naki nasan kekam bakiyi ba nace nayi mana, sai wayana yahau ringing sai naga number umma sai nace hello ummah sai yace Muhammad ne sai wani farin ciki ya lullubeni nace yayana ina yini yace kalau yace ya hanya kanwata nace alhmdlh sai yace ya kika tarar dasu nace kalau suke yace to gasu  muka gaisa dasu sai na kashe sanan naji dan sauki a raina  sai yanxu na lura Faisal baya hayyacinsa gabadaya yatafi duniyar tunani sai nace mal sai ya firgita yace hajiya mexa a dafa miki kice sai yabani dariya natashi nashga nayi wanka ina fitowa  sai yace yau ni na tuka tuwon nan da miyar kubewa nace kayi kokari yayana naci nakoshi sanan na tattara.........

Washe gari da yamma yaya aliyu ya kawo hasina sai ya tsaya a waje ashe hajiya rabi ta gayawa maamaa akan cewa Aliyu nasona zaizo yau ya sanar dani,maaamaah tace nashirya xanyi bako yau nikuma duk hankali na bai kai can ba..............
Sai mama tace hasina ki ce yaje garden tana xuwa anan hasina tashigo take cemin malama kinyi bako yana garden sai na harareta wayene plxx sai tace yayana Aliyu yazo ya bayyana miki sirrin dake ransa  sai na zare idanu tace kije mana sai na kama hanya xan fita maamaa ta kirani tace real idan kinsan bakya sonsa karki boye mar kifada mai gaskiya har cikin ranki nace toh maaamaaa...........

Na iso bakin garden nayi sallama Aliyu yadago kai ya kalleni da kyawawan idanunsa ya amsa dacewa wa'alaikissalam warahmatullahi wa barakatu ina tsaye agurin sai yace hava malama raliya tsayuwa bakamaceki ba sanan shirin koran bako ba halinki bane sai nayi murmushi na iso nazauna nace ina yini yaya Aliyu yace lafiya kalau ya kika baro su maamaa nace lafiyansu kalau sai yace  masha ALLAH sai yace raliya nace naam yace sanadiyar zuwana gareki shine naxo nasanar miki sirrin dana jima ina boyewa tunda nayi tozali dake tunani ta karkata zuwa gareki inaso naji kalamanki akan hakan sai nayi shiru sai yace raliya kitaimaki mai yawo a dokan daji yana mai jin ishirwa, sai sake cewa banji kince komai ba sai nace yaya Aliyu bangane mekake nufi sai yace nasan kingane amman kina min jan ajinku na mata ne sai yace raliya ina sonki ina kaunarki inason kizame mun uwar yarana amman inkin amince,sai jinayi shuru kaina akasa sai yace raliya, raliya,raliya yaji shru sai ya yi tafi sai na daga kai na kallesa nace naam yaya Aliyu sai yaga idanu sunyi jajur don kuka(shin kunsan kukan menakeyi??? Nasan zakuce tunanin Muhammad aaa bashi nakeyi ba to) sai yace meyasa meki raliya mena miki sai nace babu....

Nace yaya Aliyu sai yace dagata nasan zakice kina da wanda kike so,toh  naji kina da wanda kikeso raliya amman kibani dama inkasance koda na tara ne acikin jerin sunayen masoyan ki,sai nace aa yaya Aliyu ni ina da gurin kammala karatuna cikin natsuwa kar soyayya taxo ta min katsalandan .........

Sai yace bakomai real kije kinatsu akan maganan dana gayamiki tukunnan amman ina me neman yafiya gareki idan har na bata miki rai kice wa hasina ina jiranta ina tashiwa naci karo da Faisal a sume  akasa kawai sai nayi ihu kowa yafito......

Kowa yafito sai mama tasa ya aliyu ya rikeshi muka kaisa falo sai muka yayyafa mar ruwa ya bude idanunsa ya kallemu dukkan mu sai mama tace Faisal meya faru sai  yace babu komai maamaa kawai nazo xan shigo falo ne naji nafadi ban san dalilin ba sai maamaa tace ALLAH yabaka lafiya kozamuje asibiti nace aa maamaa am ok sai yatashi yanufi dakinsa yaya Aliyu suka tafi da hasina.......

Niko nashiga dakina nakwanta abun al ajabi sai naji wayana yana ringing sai nadaga naga faisal sai na dauka nace hello yaya Faisal sai naji shiru nace hello hellow shiru sai nima nayi shru sai yace kixo falo ina nemanki, sai natashi nafito ina xuwa na xauna na kunna tv ina kallo sai binta taxo ta zauna muna kallo sai yashigo ya xauna a kujera sai yace  real nace naam sai yace me Aliyu yazo yi sai nace wai yaxo gaya min yana sona sai yace kekuma me kikace sai nace,nacemar xanyi shawara....sai yace to kinyi kinyi shawaran kirashi kice an miki miji...sai na kallesa nace waye sai yace kaima haka sai nace Faisal ba shine damuwa na ba da Aliyu yasan asalina daya fasa nemana sai yace nagamar.........

Anan na basa labarin asalina dakuma abinda ya faru da yaya garba  sai yace ok kigaya mai kimai bayani sis karki boye mai domin kema kar abu yaxo yayi nisa a wargaje sai nace ok tanxx brother sai yanxu yadanyi fara a......

Ya Aliyu ya karbi number na agurin hasina yakirani anan na zayyana masa komai da komai game da rayuwa ta sai yace bskomai nabashi time amman inyi hakuri ina receiving na wayansa nace ba komai, rayuwata tacigaba a abuja amman matsalata tana tare dani missing na M da kuma kamall tsare gida sarkin miskilanci........

A kwana atashi bawuya wajen ALLAH muna shirin rubuta waec da neco mungama registration successful akan upper week xamu fara paper.............,. Ranan indo ta kirani tana kuka  gabadaya na hargitse indo meya faru tace raliya nazaci xan iya maganin abina da kaina ashe bazan iya ba nace meya faru indo tace raliya tun bayan haihuwa ahmad nafara haduwa da kalubalen gidan miji,nashiga uku indo meya faru sai tace kinga yau wajen wata uku audu baya kwana agida 😭😭 Audu sai shaye-shaye da neman mata,nace nashiga uku indo kinsan akan wa kike magana kuwa kar bacin rai yasa kima mijinki kazafi, wallahi kinsan ba halina bane raliya,hakane sai wayan ya katse

Sai na kirata da wayana yana tana ringing bata daga ba nayi wajen 10times bata daga ba sai kawai nazauna nayi shuru ina hawaye sai ga Faisal ya shigo ya tsaya yana kallo na sai yaxo yace real meyasame ki sai nayi saurin goge  hawayena nace sannu da zuwa yaya Faisal sai yace yawwa real amman meyasa kike sawa kanki damuwa real please meyasa kike boye min abinda ke ranki,yaya kamall ne? Ko nine namiki wani abun sai nace aa indo nacikin matsala nakira ta almost ten times she didn't pick the phone ok,real but why not bazaki hau sallaya kimata addua ba shine kawai mafitan mu,nace nagode yaya Faisal sai yace nima jibi zan koma Ukraine cux ana neman mu a can sai nace ba kungama ba yaya Faisal sai yace kwarai kuwa amman sun nememu ni ma bansan dalili kuma inaso kitayani addua domin nayi submit na takarduna ina nemn aiki toh yayana INSHA ALLAH sai yace to kije ki kimata addu an nima xan tayaki...........

Natashi nashiga daki bayan sallan azahar ina xaune sai nayi tunanin bari na kira umma anan na kirata take gayamin cewa suna hanyan gombe kai indo asibiti cuz audu ya mata duka hartayi bari sai bleeding takeyi kawai nakama kuka  meya faru da audu meyasamesa nashiga uku anya zanyi aure kuwa jama a kuduba yanda soyayyar indo da audu ta bunkasa amman abin haka ya koma ranan wuni nayi bana hayyacina sai ma wani xaxxabi daya zubo min sai danasha magani nake gaya wa maamaa tace zata saka ta a addua ....
Bayan magrib naji ya ake ciki tace an rikesu,bayan an sallamesu tadawo gida shine akazo aka sulhuntasu tace ita bazata koma ba da kyar akashawoo kanta ta koma yayi ta bata hakuri sanan hankali na ya dan dawo min jikina .........

Matar yayana ta haihu ansamu mace akasawa mamar su audu takwara hamsatu suka sha suna nikan bani amman hantaran yaya kamal sai gaba yake kara yi...

Munfara  waec successfully naji dadi sosai yanda muke paper ranan mun fita practical na chem sai maamaa tace yau bello bazaixo daukanki ba kidawo  a taxi nace toh mama
Munje ma kafin mufita saida muka jima wajen la asar nafito bakin gate ina jiran taxi har yan class namu suka wawwatse sai ga mal Abdullahi invigilator  namu ne, yafito yace raliya salimu ko nace eh me kika tsaya yi nace jiran taxi yace in bazaki damu ba kixo na sauke ki?? sai nace aa kabarshi kawai sai yace aa kizau na kaiki sai naje ina shirin bude motan naji ance real!!!!!!!!!!!!!¡!!!! da karfi  a hanxarce na juya waxangani yaya Faisal kawai na tsaya sai mal Abdullahi yace ki shigo mana sai Faisal ya iso yace ina yini mallan yabasa hannu sai yace mallam nine direban ta daman motan ya baci ne amman nasamu na gyara sai yace ok toh shiknan ma raliya sai kuma jibi nace thank u sir har mun fara tafiya sai yace raliya jimana sai Faisal ya wuce gaba nabishi a abaya sai yace ki bani number naki sai muna gaisawa time to time sai yace au mallam bakasan matar wani bane sai  mal ya zaro idanu how kuma raliyan kwarai ma kuwa ai anyi baiko ansa rana tana gama neco sai aure sai yace ALLAH yasan ya alheri amman wanan wani mai sa a da rabon duniya ne sai yace Alhaji Muhammad kenan yace toh amman kagayamai yana killaceta kodan saboda tsaro sai suka tafa ya wuce nima naje muka  kama hanyar gida gabadaya wata iri nake jina sai Faisal yace bakinki cike yake fal da tambayoyi zan so kiyi su,nidai ban tanka mar ba sai yaja birki ya tsaya raliya kiyi magana insamu daman baki hakuri ban kulasa ba can sai yaci gaba da tuki muka isa gida yashiga yayi parking washe gari muna gida ba paper Faisal yaxo yana ta surutai ko kulasa banyi ba sai yace mama xanje duba wancan abun nawa sai yafita sai ga text yaturo min kamar haka(AMINCIN ALLAH AGAREKI YA KE KYAKKYAWA,NASAN KINA FUSHI DANI MAY  BE AKAN NAHANA MALAMINKI NUMBER KI,KO DAN NACE KE MATAR OGA NANE AMMAN KIYI HAKURI WALLAHI ZUCIYATA BAZATA JURE GANIN WANI DANA MIJI YANA SON YI MIKI MAGANA BA NIMA BANSAN DALILI BA....amman ina mai nema gafarar zuciyar datake kunshe da yafiya....DAFATAN ZA AYAFEMIN AMINIYAR YAYA KAMALL😜take care sai na dawo)

Kawai murmushi nayi sanan wani tausayin Faisal yakamani domin nafahimci sona yake amman yana shakkar bayyana min nikuma gashi baya gabana damuwa na bai wuce na M ba shine kawai zai iya auren mara asali irinsa ALLAH sarki Faisal......... Sai nakoma daki nazauna can bacci yadaukeni

Kamar a mafarki naji maamaa tana salati tana cewa wani asibitin kawai sai nafita dagudu maamaa meyafaru sai tace Faisal yayi accident yana asibiti  nace nashiga uku maamaa muje muka fita muka nufi asibiti maamaa batasan wani irin driving takeyi ba muna isa mukaga motan sa yayi kaca-kaca mama tace Faisal karka tafi kabarni irin na Sabeer, kawai nabi bayanta da gudu akace suna emergency mukashiga word din kawai sai ga wani anrufe shi da farin kyalle anfuto dashi akan gado maamaa tayi kan gadon da gudu sai doctor yace kune yan uwan Fa...kawai sai maamaa tace eh mune sai yace am so sorry to say kawai ta wankesa da mari takama kuka,sai yace hajiya kiyi hakuri
 ALLAH yamasa cikawa  sai maaamaa ta matso kusa da fuskan tana budewa taga fuskan yayi raga raga baza ma kaga ne waye bane tuni nayi dogon suma maamaa hauka ne kadai batayi ba  wasu mata suna gefe sai hakuri suke bata niko tun yaushe aka kaini wani daki ana treatng nawa maamaa hauka ne kadai batayi ba tsabagen rikicewan datayi
 mama tana xaune bakin emergency sai taga inuwan mutum akanta yace maamaa sai kawai ta firgita wa zata gani sai faisal da bandaji akai.
Tace Faisal yace naam maamaa sai ta juya taga wancan akwance akan gado sai ta mike tsaye yace maamaa sai ta rungumesa tafara kuka sai ga likita ya fito sai yace hajiya kuyi gaggawa adaukesa sai tace ba dana bane doctor ganan dana sai yace ok ke Faisal ne danki tace eh,sai yace hajj amman kema bakijira na fada miki sunan bane amman wannan ai fahad zaki ne........ Sai kawai tayi salati tamai addua sukama nurses suka wuce   da wancan gawan zuwa dakin mamata sai tajuya tace faisal ya akayi sai yace maamaa nima on xpectd  jinayi na buge wani karfe... kawai farkawa nayi naganni anan sukayi ta godiya wa ALLAH  sai yace maamaa mutafi sai tace real na ciki tayi dogon suma saka makon ji tayi ance karasu😭😭 sai gabadaya yaji shi ya warke sumal fatan sa real ta farfado can wata nurse tafito tace xaku iya shiga....... suna shiga kawai naga fatalwa  nabin bayan mama atake nafara surutai nace faisal kayafemun  kadaina mun gizo sai maamaa tace wannan fa faisal ne domin bai mutu ba wani farin ciki ya lullube ni na tsinci kaina ina maison jin sautin muryansa shikuma bayi magana ba sai nace yaya faisal sai yace my little real sai na ce naam daman kina sona kuma kindamu dani??? Sai nace sosai ma yayana yaya jikinka Alhamdulilah da sauki sai yanxu mama ta lura takalmin Kamall  ne a kafarta dakuma yadin dinning table sukayi ta dariya.....
 Can bayan la asar aka sallameni muka koma gida nida su mama

Mu ka iso akasanar da yan uwa har mummy daga niger tazo ta dubasa duk da maamaa tahanata amman hankalinta bai kwanta  rayuwa mai dadi nakeyi idan yaya faisal nagidan..................................mun gama waec namu saura mana days mu fara neco aka aiko faisal yasake komawa ukrain ana neman ranan da zai tafi kawai ya rinka kuka yana neman yafiya kamar wanda mutuwa xai yi nima har na karaya nafara hawaye muka rakashi har airport muna hira sai ya kirani gefe yadau wani zoben azurfa sai sheki yakeyi yace gashi nakarba nace wannan kuma fa sai yace barka da ranan haihuwarki yer uwa kawai sai natuna ashe yau birthday bansan lokacin danayi ihu ba har maamaa tamin fada yace naji haushin tunda kike baki taba celebrating ba naso namiki sai gashi an neme ni but promise to do so indawoo kinji real nace toh na amsa muna ta hira can suka tashi muka rabu dashi muka komo gida.......

Ranan talata maamaa tayi shirin tafiya wudil ziyara tabarmu a gida tun lokacin data ambaci tafiya zuciyana ya tsinke gabana yacigaba da faduwa sai dai binta nagida sai nace maaamaa ki kaini gidan su  hasina tace aaa nasan matsalanki  kamall ko to karki damu nagama magance miki matsalar ki tuntuni domin akwai kanwar mahaifiyarsu uwani tana suleja zatazo ku zauna kafin nadawooo baifi kwana uku xanyi ba real ki kwantar da hankalin ki kinji ko nace to maamaa nagode natashi na nufi daki ina mai kara jaddada godiyana wa mahaliccina......

Ranan alhamis da sassafe maamaa takama hanyar zuwa wudil aka barmu da uwani,,,uwani tana da kirki ga son barkwanci tana bani labarin mijinta yarasu yabarta da yara amman alhmdlh tana kula dasu baruwanta matan har nake sakawA araina dama kamall yabi halin babarsu nan daya more rayuwarsa,,munyi kwana biyu da tafiyar maamaa sai naga uwani tafara dauke mun kai kamar bata sanni ba kawai nima na watsa kashinta sai karatun paper na nakeyi ranan litinin dasafe nayi shirin fita skul yaya kamall ya kirani yabani wani field sai yace real ki ajiye wa maamaa file dinnan kinji ki ajiye inda bamai tabawa sai ta dawo
Nace to nikuma gandan komarwa ciki nake domin nayi late kawai natafi dashi skul mukaje mun fito daga obj before mukuma essay sai nasaka a jakan hasina har aka tashi na manta sai danazo gida tayi min waya take sanar dani nace shiknann ki ajiye amana ne plsss karkibama kowa kinji sai na nema  shiknann sai yaya kamall ya kirani ina file nayi mai bayani sai yace kinsan file dinnan nameyene nace aa yaya sai yace fili maamaa tasaya akeso akwace shine orinal copies nabaki kiboye karki nuna mata nina baki kinji sai nace meyasa sai yace nayi miki alkawarin jin dalilin amman bayanzu ba kirike amana to insha ALLAH nayi mai sai da safe nashiga na kwanta

RANAN TALATA maamaa tadawoo niko nariga nakarbi file din naboye a kasan kayana maamaa tadawo muna ta murna ashe bansan nawa murna zai koma ciki ba washe gari laraba muna da pratical amman sai  12 don haka na baje ina bacci na sai ji nayi motsin mutum akaina ina farkawa naga maamaa a tsaye da file a hannunta yayakamall da uwani da binta sai kawai na firgita danaga file a hannun maamaa sai nace yawwa maamaa kawai sai ta daga min hannu danufin indakata sai najiyo murya hasina afalo tana nufo dakin mu sai   tashigo itama ta tsaya sai maamaa tace naji dadi dakika zo hasina duk irin kyautata wa raliya danakeyi ashe cin dunduniya ta take yi sai nace maamaa mena miki sai tace ta daga file sama ta nuna min sai hasina tace karde abune yabata aciki kingada kinbari na ajiye agurin nawa dahaka bata faru ba sai maamaa tace me kike nufi kinsan file dinnan tace tabbas mama domin real tabani amarnarsa ya kwana agurina jiya ta karba sai kawai suka doka salati sai
Maamaa tace sauko tafito da akwatin kayana ta xuba kayana aciki tadau dubu goma ta watsa min kijena sallameki bansan lokacin na fara hawaye ba ina maamaa mena miki maamaa ki taimakeni naje gaban kamall na tsuguna ina kuka nace yaya kamall kayi ma maamaa bayani don ALLAH sai ma hankade ni yayi da kafa,,hasina taxo da gudu takamani tafara kuka kiyafeni bnsan fadin magana zai jawo miki matsala ba taje gaban maamaa tana kuka maamaa karki kori raliya kiyi hakuri kawai fita tayi dataxo bakin kofa ta juyo tace raliya nabaki minti uku kibar gidan nan kafin nasa amiki najaki sai na tattara kayana namaida mata cikin drower nata daman anan na samesu to anan xan barsu na dauki kwalin wayan da faisal yasamin na mai da komai da komai sannan narubuta mai saduwar alheri ku yafemin ina fatan kai baxakq kasance cikin masu zargina ba natashi nadau dubu goman na fita ina kuka hasina na biye dani tana kuka sai tace

Raliya raliya nace naam ina kika dosa nace mata  gombe kauyen mu nafada tace aa wallahi muje gidan mu tir na turje naki yarda tama ya aliyu waya yaxo har mamansu suka sani dole na bisu mukaje sai hajiya rabi tace kina gidan nann sai kin gama paper sanann aliyu ya maida ki gurin iyayenki sanan nima daga baya nazo na nemi izinin kasancewa agida na kinji nace to ina ta murna amman a fuska domin tunani yafi karka ta akan mena ma maaamaa tayanke min danyen hukuncin nann

Nayi kukan zuci har na gaji akan meyasa kamall yamin haka kodan ma da haushinsa tunda amman idan shi da haushinsa to mena ma baba uwani???wayyo ni raliya kawai sai natuna maganan ustaz kabir sai na kama INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU.UN
Can kamar daga sama sai naji ya aliyu suna magana da su hasina yana cewa shiyasa fa real take burgeni saboda tsantsanyar tawakkali ga ibadah sanan nadawo daga duniyar danatafi na tunani

Kai rayuwa tamin dadi agidan su husna suna min soyayya nakin karewa sanan suna min kulawa sosai amman dai duk da haka ban manta da rayuwan gidan su maamaa ba domin itane jigo na data fara sakani a hanyar karatu ta kaunace ni,wayasani ko faisal yadawo gashi kuma ko nema na baiyi ba toh ALLAH yataimakemu AMIN.......


Acan nafada kuwa audu yayi wa saddiqa ciki labari duk ya zageye gari gabaya audu yacanja hakan yasa indo tashiga duniya inda aka nemeta aka rasa karshe ma saddiqah ta tare tadawo gidan sa da zama,mahaifiyarsa tayi kuka tayi nasiha har ta koma ta fawwala wa ALLAH komai sai addu a ake masa

Hmm ba anan gizo ke saka ba ashe ni ina can ina gina soyayyar muhd a zuciyana shiko yana nan yana soyayya da talatu kanwar indo😱..........

Nagama paper na lafiya kalau mukayi candy ba abinda hajiya rabi da danta aliyu basu mun ba gaskiya sun cancanci abin yabo bayan cenforth namu nafara shirin komawa gida domin na masu naga M, Ranan Lahadi muna hira harda abban su hasina.................
sai abban su hasina yace na shirya ranan talata ALIYU ya maidani sai  nace toh bakomai sai umman su hasina tace aa bazaiyu ba ni yakamata na maidata naje namusu bayani ai yafi ko in sun amince sai mu dawo tare a fara jiran fitan result domin a neman masu high institution ko sai yace ok ba komai bari zanyi wa  Alhaji Abdulkadir waya friend nawa na Gombe sai kawai kubi flight dukanku kuje nikuma zani kano ziyara sai kuje ku kwan biyu kudawo kunji sai sukace toh farinciki har raina,,sai naji Aliyu yace Abba kawai sai naji zuciyata ta buga sai yace menene Aliyu sai yayi shru sai hasina tace nasani abba sai yayi wuf yace daman abba abokina Aminu ne yakeso a bashi ixinin magana da hasina yajima yana min magana amman ban kulasa ba toh jiya yake gayamin ma wai zai turo iyaynsa anaima mai ixinin magana da ita hava tuni hasina taruga da gudu taje dakinta sai kawai suka kwashe da dariya
Sai Abba yace kace mai toh gobe ya turo su ina nan around 2:00 haka sai yace toh Abba sai muka musu sai da safe muka nufin dakunan mu na isa nasamu hasina na kuka hasina meya faru sai tace kiga abinda  aminu zai min mena masa zai saka min da wannan sai tasake fashewa da kuka sai nace kina dawani saurayin ne hasina koba kyason Aminu ne sai kawai tarumgumeni ta fashe da wani dariya tace real niko nakeson Aminu Domin aminu yayi a rayuwa kukan farin ciki nakeyi real shi duniyar masoya bata gama cika har sai kasamu mai kaunarka don ALLAH kawai sai naga ta mike tsaye tace real aminu tun ina yarinya yake min tsokanan mata ta alokacin dana fara girma naji duk duniya bawanda nakeso irinsa amman bansan ya xanyi ba haka na danne kayana na hakura ashe shima sona na ruruwa azuciyarsa irin nawa kawai sai yau naji magana ta fito Alhmdlh sai ta juyo tace real idan har aminu xai fito da maganan aurena a yanxu toh wallahi bazanyi karatu ba sai dai nayi agidansa niko gabadaya mamaki yakamani nace daman hasina kina soyayya sai kawai tace min kwanta kiyi baccinki nikam sallah zanyi nagode wa ALLAH daya cika min buri a takun farko kawai tashiga bandaki niko nakama addua nayi bacci

 Washe gari dayamma muka fita shopping dasu umma anan tace muje mu sauketa agidan su maamaa mukaje mukuma muka wuce shopping tare daya Aliyu da husna muna can sai ga Aminu tamkar daga sama aka jefosa yazo suna ta tsokanan juna da Aliyu sai mukaje mukayi hanyar mu nida hasina, sai hasina tace kiga al amin nawa ya biyo ni sai nayi dariya sai tace ALLAH fa ina sonshi amm yawwa dazu da su babansa sukazo plxx me sukace kawai sainaji murya a bayan mu sunce aminu naneman ixinin  magana da hasina sai akace anbashi yaje yanemi yardarta kawai mukaga Aminu abayan mu na kora jawabi sai hasina ta juyo a hankali ta kalli aminu shima kuwa kur idanunsa acikin nata kawai naga sun tsaya suna kallon juna tamkar babu rayuka ajikinsu aliyu yazo yana ta magana shiru daga kan dazaiyi yaga sun daskare suna kallon juna kai àminu kawai ya jijjiga ya biggeshi da mukulin mota... A rikice sai yace naaam hasina hhha kawai muka kwashe da dariya sai  Aliyu yace Aminu kaikam ba a shago fa muke sai yace toh haramun ne matata ce fa sai yace kace (to be) bawai matarka ba tunda bamu shafa ba sai yace naji ni ansan inayi ansan dani wani da yake beating around  the bush fa, sai aliyu yawuce bayi magana ba sai nace aminu kenan a sannu jeji kedawowa birni matsugunin jama a sai naga aliyu yajuyo yace ah toh real fada masa dai  sai dukan mu muka kaure da fara a muka gama siyayya harda kayayyakin tsaraba na anan akasayamin new phone mukaje biyan kudi aminu yatirje wai shi zai biya ya biya muka fito sai aminu wai shi zai dauki hasina aliyu yace sam yanda mukazo haka zamu koma sai nace ya aliyu kabar mu mutafi gida da aminu da kayan inyaso kai kaje kadauko umma agidansu kamall sai yace bazaki rakani ba kenan nace aa bnson komawa gidan kawai kaje sai yace shiknan nagode muka yi hanyar gida shikuma ya wuce dauko umma.....

Abun mamaki muka dawo muka tarar da umma agida sai abin ya bamu mamaki...sai nace umma mun tura ya aliyu yaje daukanki fa sai tace eh kawata takini sanadiyar nakawo ki gidan nn duk jikina sai yayi sanyi muka iso umma meyafaru? danaje take ta fada wai meyasa na dauki barauniya kamall yagaya mata kina nan domin har cenforth naku yaje sanan tace ita ba ruwanta idan kika min irin abinda kika aikata mata shine nima na tattara nafito nahau taxi nadawo randa ta huce na koma mata domin ga dukkan alamu kamall na zugata sosai .......................
sai kawai nafara hawaye sai umma tace meyasameki real sai nace bbu sai hasina ta dafeni tace kiyi hakuri real ki share hawayenki INSHA ALLAHU kinsamu yen uwa na har abada domin bazamu taba rabuwa dake ba.....
Sallamar abba yakatse mana maganan mu yashigo yasanar damu gobe kar 10:30 jirgin mu xata tashi zuwa Gombe nayi farin ciki sanan abba yace idan kunje kun huta a gidan Alhaji Abdulkadir sai jibi kidau hanyar nafada zai hadaku da drivern sa mukayi godiya sai ya juya yanufi dakinsa sai ya juyo yace hasina tace naam abba sai yace kije aminu yaxo yana falon baki sai nace  ai kawai tayi wuf ta rufe baki na sai abba yace meyena sai umma tace tare sukazo domin aliyu yaje daukana sai kawai yajijjiga kai yanufi dakinsa muma mukayi dakinmu mukayi namu dakin........

Nakama shirya kayana sanan na hada sabon waya na da sim sai na dubi hasina da zummar yi mata magana naga kwata kwata bata ma cikin hayyacinta hankalin ta yana kan madubi tana tsara kwalliya sai nace malama sai ta juyo yane real nayi  kawai murmushi nayi nace sosai ta tashi tace natafi falon bakin my one and only is waiting for me xata fita na fizgo ta hava hasina ya za ayi ki zama haka kamar ba mace ba atleast kidan ja ajin nan mana sai tace keh bar ni inason abina naja aji nashiga wahala wallahi bazanyi ba sai nace ok but bnda saurin baki kafin yace yana so ke kifada sai suka kwashe da dariya ta fita niko naci gaba da aikin gabana


Chan bayan la asar aminu yatafi muna zaune da mutumiyar tana bani labarin  al amin nata sai umma takirani muka hau tayata shirya kaya a kwati muka gama sanan muka dawo falo  sai ga ya Aliyu ya shigo muna ta hira aka kira hasina a waya sai ta tashi sai ya Aliyu yace real nace naam yace ina maganan mu ta kwana sai na tsunkuyar dakaina sai nace havaa Ya Aliyu kawai mukaji sallamar umma sai natashi nashi dakin mu ..........

Ranan talata 10:00 cif muna airport muna shirin zuwa gombe by 11:30 muna gidan ALHAJI ABDULKADIR dayake GRA aka tarbe mu cikin murna da farin ciki tamkar mun shekara da sanin juna......

ABDULKADIR AHMAD yana da yara takwas na fari twin ne Hassan da Hussain san an yasir sai kuma zam-zam sai kuma still twins mata Nafeesa da safeena sai kuma walida sai afnan yer auta Matarsa daya ruwansu gwanin sha awa .......

Zam-zam yanda kasan tasan mu tunda can takaimu dakin ta muna zama sai ta nuna hasina tace ga raliya ga hasina sai mukace baki ci sai tace najuya mukayi ta dariya gwanin sha awa nikam rayuwarsu tamin wallahi abincin dare tare baki daya muka ci a tray daya mu matan suma haka daddynsu da mazan
Muna ta hiran mu around nine kawai ummu (hajiya rabi) tafara amai da gudawa aka tattarata sai hospital aka bata medicine sukace chanjin ruwa ne....Bayan sun dawo take cemana gobe da Aliyu da hasina su rakani gida suga inda nake inyaso sai insun dawo kafin nan tasamu karfin jiki sai taje cuxx yanzu batajin kwari ajikinta kwatsam kawai yasir yace to umma su zauna mana inkinji relief sai ki tafi ai nan ma gidane
Sai tace aa yasir kar hankalinsu yatashi gwara ita sukarasa sai nace to umma  sai yasir yace toh nizan kaiku kunji sai mamansu wanda suke kiranta da Ammi sai tace yasir kafiye kazazzabi sai umma tace kyalesu halinsu ne dukansu. Mukaje mukayi bacci gari na waye wa around 8 muka kama hanya sai yasir yace amman in munje kwana zamuyi nace duk yanda kukeso idan zaku iya kwanan kauye toh shiknan sai zam zam tace ai kowa asalinsa kauyene.......

Sai yasir yake bamu labari akwai lokacin wai yana hanya zai raka yaya hussain lokacin sunzo daga london wai ganin kauye kawai sai mai yakare mana a jeji muna tsaye mun rasa yaxamuyi kawai sai mukaga wani bafulatani mai kiwo muka cemar ko yasan inda xamu samu Mai sai yace muxo muje mukadau galan yasaka mu a bayan amalanke yaya hussain sai surutu yakeyi kunsan me wanan mutumin yamana duk sai mukace aaa sai yakaimu rigarsu ga uban nisa sai yakawo mana man shanu😁 Hussain suma ne beyi ba kawai suka kama dariya hasina harda hawaye sai Aliyu yace yakuka kare sai yasir yace amalanke mukace ya maidamu yace yasin bazai maida ba da kafa muka fito.........   Hava sai dariya muko muke ta musu.................

Sai hasina tace ya kukayi kuka samu Mai sai yace waya mukayi akazo aka kawoo mana ai muna koma gida ya hassan da hussain sukace Nigeria ba tasu bace suka ware haha duk sai dariya muke sai yace raliya sai hasina tace real sunanta oh awww real ta ina zamu bi ne sai nace ashe ma kasan garin sai nace kabi tanan ina nuna mai tsaf gamu a kofar gidan mu ...
Abba nazaune muka iso kusa dasu mukayi parking muna sauka sai ga call na umma mukace mata mun isa yan xun nan tayi murna tace mugaishesu.......
Muka isa sai naga Aliyu yana ta kallon abba sai yace kamar nasan wanan mutumin a wani guri amman na manta but his face luk familiar to me yana gayawa yasir kawai sai suka basar  da maganan muka shiga ciki aka tarbe mu hannu bibbiyu nakai kayansu dakin baki sanan nakaimusu abinci anan na kece musu sai dai kuyi hakuri kunsaba da A.c gen bed to nan babu sai aliyu ya harareni to sai me muma nan gidan mu ne sai yasir yace dazaku taimaka dakun ban daki daya nadawo nan da zama domin kauye na masifan burgeni su umma farin ciki ganina harta rasa nayi.........
 Bayan Sallah la asar ne Aliyu da yasir suka samu Abba a zauren gida suka iso sai yace yen samari kunsha gajiyan hanya  suka gaisa yatambayi sunayensu suka farfada mai sannan Aliyu yafara korawa Abba bayanin abunda ya faru a abuja abba har da hawaye yana ta musu godiya sanan yasa aka kira umma  yake maida mata zancen sai wayan Aliyu yahau kida an kirasa sai yace abba zan dauki waya sai ya dan tashi ya shigo daga ciki yasa wayan a kunnensa sai yace kaji sarki mai mata daya dan sarki jikan sarki takawarka lafiya  shiko sai dariya yake yace aliyu duk kun kimu ko irin wayan nan ma babu  ina hasina nace lafiyan mu kalau ina umma kuma ita tana gombe mukuma muna nafada
Sai ya maimaita nafada kokaje neman aure ne  aliyu shegen kaya sai nace kusan hakan ne sai dukan mu muka kwashe da dariya Takawanka lafiya sai gani da zam zam da kuma  hasina mun fito zamuje ziyara sai aliyu yace ina xuwa sai nace xamu dan zagaya ne tunda rana ya sauka sai yace ai sai ku jira mu mutafi tare sai sani yace kai shegen kaya bani budurwan naka mana mu gaisa tuni aliyu yatafi maganar xuci toh yanxu inna bata ta wulakantashi fa hmm gwara ma fa na share sa zai fi sai kawai yace kabata man romeo hankalinka duk baya jikinka sai yace hasina ga yayanki ku gaisa mai sunan sarki ne sai hasina ta amsa sai tace yaya sani da girma kujeranka sai yace amaryata kinshirya ne nazo da kayan tambayana sai tace tabbdi me xanyi dakai ai yanxu kazama old fashion mu sai sabon jini sai ya kwashe da dariya lalle kam yan mata an girma.... sai yace ina budurwan aliyun bata mu gaisa sai ta miko min aliyu kuma yana kallon ikon ALLAH  sai na amsa nace Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu sai ya amsa da daura da masha ALLAHU kice wanda Aliyu zai aura kawai sai nayi yake domin harga ALLAH maganan baimin dadi ba sai yace ALLAH yasanya Alheri nace amin na mika musu wayan Daga ganin aliyu kasan yashiga farin ciki sai ya amsa saiga umma ta shigo nace umma bari mudan zagaya gari tace toh babu komai sai muka fita.......... zam zam takasa rufe bakinta sai cewa takeyi wallahi kauye yayi nifa inason kauye sai hasina tace real ki nema ta miji kawai nace angama sai muka hango dandaxon yara da yan sanda damasu kama yan shaye shaye,sai yasir yace meye wannan kuma???sai nace wayasani muka tsaya a gefe muna hango abunda yake faruwa mutane ne ake dukan su ana dura su a mota can wa zan hango sai naga Audu a cikin motan an nufi gombe da su......
Kawai hawaye a idanuna sai na tuna audu mai mana nasiha ALLAH SARKI DUNIYA 😭 yanxu ko wayasan inda indo take labarinsu kamar ba ayi ba sai na goge hawayen idona sai dukansu suka watso tambayansu  lafiya???????

 Nace lafiya kalau mutafi kawai yasir yace kifada mana idan da matsala nace babu sai Aliyu yace look real ya xaki daukemu mu fito tare ana nishadi ki sauya lokaci guda kuma kice kar mu damu zancen kikeso ance da gauro ya iyali sai yasir yace kai kenan sai dukkan mu muka haure da dariya sai nace muje xan baku labari wan nan da yan sanda suka sa a mota nan nakarshe ai.... Wuf hasina ta karba ai saurayinki ne ko,,,? ALLAH ya kiyaye inji zam - zam ai real ba kallan yan garin nan bane, sai yasir yace kallan mu ce sai zam zam tace kallan ya Ali dai nidai ko kala bance musu ba
Sai danaga suna tayi sai aliyu yace kubari abamu labari duk kun katsar mata da baki sai ya ce real muna jinki sai nace shine audu mijin kawata data bata ba a ganta😭 duk sai sukayi shru    sai suka fara nemamai shiriya da kuma ALLAH ya bayyanar da indo nace amin nagode
 mukaje gurin dandali mukaga ana ta gyaran gurin anan naga buba abokin audu na tambayesa meyake faruwa yace yau ne nafada xata fara bikin shekaranta 50 da kafuwa sai nace toh najuyo na sanar dasu...  Woooo bakin yasir kamar xai yage yace mu koma gida anjima mu dawo nace

Muka dawo muka tarar umma tamana tuwon laushi miyar kuka kuma ta dama na fura da nono nikam naga ikon ALLAH wato su hydar cin dasukayi ko agidansu albarka ina dar dar dazaman su amman su sunfini ma sakewa sai naji wani dadi ya lullube min xuciya  muna ta hira bayan munyi jam i na sallan isha sai yasir yaji kalangu yace kaii ku tsaya muje dandali sai ko duka mu  muka tuna da xuwan mu can muka shiga dauko mayafi muka fito har mun je kofa nadawo sai suka tsaya suna kallo na nace umma ina ya Muhammad ne sai tace  awww na manta ban gaya miki ba yatafi gombe amman yau zai dawoo insha ALLAH nace meyaje yi tace yaje saro wasu kaya wa mai gari ne kinsan gobe akwai hawa saboda murnan shiga shekara hamsin da kafa garin nan sanan kuma za ayi auren yaran liman hasan da hussain nace toh
 na wuce mukaje dandali ana ta kidan kalangu ana rawa, yan mata da samari sai yasir yace nima fa inaso nayi rawa sai kawai natafi naje gurin mai kalagun nabasa dubu daya nace ga baki sunzo garin nan suna so su shiga fili aiko tuni yafara sanarwa harda kiran sunayensu suka fito aliyu kam yaki akasa kalangu kidan SABADA hava mexan gani yasir har kasa ya na rawa hasina kuma tana ta azonto don dariya kamar nayi yaya kowa agurin sai dariya akeyi kwatsam gulma yaje gun mai gari basai gashi da fadawa sunxo kallo Aliyu yana ta daukawa a wayarsa.  sai aka kashe kida yasir harda bata rai sai mai gari yace agayawa wa mai yekuwa yasa ayi shuru!!!

 Sai yanxu yasir yasan ma suwaye agun sai mai gari yace yaji dadi ya kuma nisha dantu da wannan rawa da yaron nan yayi don haka anbashi kyautar SA   guri ya kaure da ihu sai tafi ake tayi
Sai aka cigaba dasa ka kalangu aka cigaba da rawa sai yasir xai je aliyu ya hanasa yace dawo dan mazari anbaka saniya bai isa ba sai an baka mai garin tukun xaka hakura sai yafara  gunguni sai ya hakura ya tsaya amman jikinsa na rawa shi kadai
 sai zam zam da hasina suka ce ke ya kin wani makale bazakiyi rawan bane sai nace bana rawa sai inji yasir idan bakiyi ba mungane ke budurwa Aliyu ne shiyasa kika kiyi don yaki yayi sai na bisu muka je muna tayi sai hasina tadawo wai ta gaji muko muna ta rawa kawai sai hasina ta ga wani abin al ajabi sai murza idonta takeyi domin ta tabbatar da gaskiyan lamarin batama kara hauka cewa ba sai dataga yaje kusa da raliya suna magana tuni tayi ihu tafadi a sume mukayo kanta da gudu ya M yakawo mashin nasa yadaura ta akai muko muka bisu sai gida muka iso hasina a sume aka yayyafa mata ruwa tana farkawa taga kalle mubaki daya har ta tashi ta xauna muna cewa sannufa sai ta sake kwala ihu ta suma ni nafi kowa gigi cewa sai yasir yace y not mu dau mota mu koma gombe nace dayafi ai yasir yaje daniyar tada mota yaga ba mai ohhhhh yadawo yasanardamu

Sai ABBA yazo yamata tofi a ruwa akayi mata addu o i tanan farfado amman bata magana sai kallo muka ma hajiya rabi waya muka gaya mata tace tana nan tafe da likita gobe da ammi  umman su yasir ranan kwana zaune mukayi kowa kagani banda tsoro da tausayin hasina ba abinda xaka gani sai karfe biyar na asuba tasamu bacci mukayi sallah mukadawo kanta muna addu'a,
 Su umma sukayi waya suna hanya sai mukace toh baba zuwaira da umma na sukayi kokarin hada mna kumallo misalin 8:30 sai ta farka tayi wanka mukawo abinci muna bata sai abba ya aiko M daya kawo mata rubutu tasha yana zuwa suna hada ido tasake kwalla ihu ta suma sai muka sake hawa kanta da fifita muna ta addu o i can karfe 10:00 sai ga su umma sunxo sunxo dai dai lokacin kuma umma da abba sun tafi gurin mai gari ya ara musu mota muje asibiti don jikinta yaki muka kawo musu ruwa suka sha doctor yafara dube dube akanta sai ga Muhammad yashigo yana tambayan ya jikinta suna hada ido da hajiya rabi tuni ta yanke jiki ta fadi hava yasir ya daka tsalle ya cukumi wuyarsa .................................

Acan kuma birnin tarayya tun bayan barina gidan kamall gurinsa yacika nagani. An korani daga
Gidansu balkisu taxo daga kano dataji labarin abinda yafaru tayi ta kuka sanan tabar ma gidan ta koma gidansu da zama kamall inyaje bata fitowa anyi anyi tadawo taki
 Akwai ranan wata talata kamall yaje hira gunta kawai yatarar da ustas kabir suna hira tare kamar ya hadiye xuciya ya mutu haka yadawo gida harya hadu da hawan jini..........

Ranan wata jumma a faisal yadawo daga Ukraine tunda akaje taransa a airport yake tambayar ina raliya??  Amman babu wanda ya kulashi bayan sun iso gida ne yayi shru da tambayarsa domin  anashi haukar tana nan,  yayi wanka yaci abinci yayi sallah yayi addu o i kamar yanda yasabaaa

Sai yafito falo suna ta hira da mutanen gida sai yace maamaa ni raliya ta tafi girinsu ne ??cewa tayi eh tana mai kallon fuskan wayarta batare da ta dubesa ba sai yace ina neman layinta baya shiga ko ta sauya layinta ne?  Nan ma maamaa kawai Eh tace mar fuskanta ba fasaha shi yanayin amsawan maamaa yafara bashi tsoro jiki ba kwari yakuma cewa maamaa toh abani sabon layinta mana ,  kawai tashi tayi  tashiga dakinta ta manta da kashinsa shikuma abin yana bashi maamaki,,
Yana zaune agun jikinsa ba kwari yana ta maganar xuci Sai ga uwani taxo yasauka a kujera suka gaisa sai take cemar toh faisal kasan tun kafin fatsuma ta rasu (maman su faisal kenan) kasan tace tanaso ko kai ko kamal dayanku ya auri daya daga cikin yarana toh abinda yasa nazauna najira xuwan ka shine munyi maagana da mamaa akan ahada ka da harira yer wajena tunda  shi kamall ya fito da balkisu kaga sai muyi tuwo na mai na(dakan daka, shikan daka,  tankaden bakin gado)....
 Sai yayi wani doguwar ajiyar zuciya ya ce baba uwani a zahirin gaskiya ina da wanda nakeso kuma nariga dana tsara rayuwata da ita xanyi ban taba tunanin wata 'ya mace ba sama da ita kuma kusan nan xan tada maganan auren mu da ita sai uwani tace yer waye ne wan nan sai yace yarinya ce mai tarbiyya da sani  yakamata ga addini ga asali ga  kyau ga hali me kyau...
Tun wata zuwata nigeria danaje katsina hutu ina dawowa dana daura idanuna akanta xuciya ta ta amsa tayaba ta kuma amince alokaci guda nakasa na tsare naji inba ita bani kawai...
Sai uwani tagyara zama 'yer gidan wani ALHAJI NE tayi awun gaba dakai dayawa sai yayi murmushi sai yace raliya ce........
Sai  baba uwani tace wani raliyan ta watso tambayanta tana mai turnike fuska sai yace uwani bakisan raliya yer gidan nan ba? sai tace dakata sha sha sha kawai yer aikin gidan nan din xaka aura????  Kamar a sama yaji ana cewa bana gaya miki ba baba uwani juyawan daxeyi yaga kamall yana shigowa kawai suka taru suka haushi da fada, Ana cikin haka sai maamaa ta fito a dakinta sai yaji sanyi a ransa anashi tunanin xata goya mai baya yayi wuf yacee maaamaa kece uwata kixo kisa baki akan abinda yaya kamall da baba uwani kefada budan bakin maamaa tace nagode wa ALLAH dakasan cewa ni mahaifiyar kace sanan nasan kasani wanda ya sabawa mahaifiyarsa ya makomarsa take..  ta iso ta zauna akan kujera ta kalli faisal tace faisal banyadda ka auri raliya ka kawoo mana ita gidan nan amatsayin surka ba..  Bada yawu na ba idan kuma har haka takasance kanuna min cewa ni bani bace mahaifiyarka.....................  wani hawayen takaici suka makale a idanun Faisal sai yayi ta maza yace maaamaa me real tamuku wace irin laifi ta aikata haka har ke da kanki kike wannan batu akan sai maamaa tace bari na gaya maka raliya munafuka ce......... ,kuma yer iska ce inji kamal...  haka zalika barauniya ce inji baba uwani anan uwani takarba ta fara juye masa bayanan karya da gaskiya.........
Hmmmmm SO kenan suna jawabinsu amman shi lokacin ma yaji sonta da kaunarta na kwaranya a xuciyarsa.. Uwani tagama sai ya kalli maamaa yace maamaa yanxu ke kina da tabbacin raliya xata iya wannan ta asar kawai tsoka taja tace sha sha sha sakare. Imma asirceka tayi dole ka rabu da ita suka watse suka barshi shi kadai a falo yana xaune yana karanta wasikar jaki can yaga baci sai ya shiga dakinsa ya dauro alwala yayi. Sallah sai yayi addu o i  anan yafara tunanin meye mafita kawai sai wata dabara ta fado mar

 Ya dauko wayarsa ya daura a kunnensa can sai yace kina gida ne, sai kuma yace gani nan xuwa sai ya kashe yadauko key na motarsa ya fito yana xuwa dai dai motar yaga tayoyi duk a sace sai yajuya da niyar karban motar kamall sai gashi suka hadu a kofa sai yace yawwa ya kamall bani motar ka mana xanje nan kusa na dawo sai yace xan fita sai yace ok ajiyeni mana ko abakin titi nahau taxi.  sai bai kulasa ba ya nufi motarsa shikuma faisal na binsa abaya yana zuwa daf da motan sai ya juya  ya ce hold on i cnt pick u faisal xaka iya bin taxi.........  kawai yaja motarsa ya fita faisal ya bushe a gurin tamkar ba jini a jikinsa karan wayarsa ya dawo dashi daga tunani ya dauka yace yane aminu suka gaisa yace eh ina gida ok sai ka iso

Baifi minti ashirin ba sai ga motan aminu a kofan gidansu yayi wuf yafito yace aminu kaini gidan su balkisu  mna sai yace ha a ba a gidanku take ba? Sai faisal yace aaa taje kwana biyu wa ummarsu sai yace ok kawai yaja mota suka nufi gidan su  balkisu yana xuwa yaga motan kamal  a kofan gidan sai yace aminu yi gaba kadan yayi parking gaba da gidan sai fasail yamata waya tana fitowa taga kamall sai shikuma har da fitowa yana ta burga a dole shi mai budurwa ta doshi gun motan data ga kamall ta bata rai sai ta dago wayanta da niyan kiran faisal sai kamall yayi wufff yace gani nan fa sai kawai tsaki taja sai faisal yafito yace gani sista sai ta isa gun motar su tace su isoo gida tare da aminu tayi gaba suka bita abaya kamall yayi sololo ya rasa me ma zaiyi don bakin ciki sai yayi ihu yace faisalllllll xaka dawo kasameni. Bai gama kalamansa ba yaji karan Achaba a gefensa juyawan da zaiyi yaga ustaz kabir na kokarin parking sai ya juya yakallesa sama da kasa yace imba balkisu da rigima ba meya hadin BIRI da KADA  menasama yaci da zai bama na kasa mtsw........ sai USTAX KB yace  hmmm ALLAH UBANGIJI YA SHIRYE  KA ,,,,, kamal Ya hasala ya kaimar naushi ya gauce sai yakama hannunsa yace kamall ni ba sa anka bane sai yawarce hannu tuni ilu mai gadi yaje yasanar ma su. Bulky abinda ke wakana a waje balkisu na fito dai-dai da kamall ya wanka ma uztaz mari yana shirin ramawa tayi gudu takame hannunsa sai ya ce A UZUBILLAH sai wafce tace ustas kayi hakuri INNALLAHA sai karasa dacewa MA ASSABEERIN sai tajuya ga kamall tace bar  kofan gidan mu a fusace yashiga motansa yace kina shirin jefa kanki halaka ya fizgi motansa yayi gaba sai lokaci faisal ya karaso gurin  domin yasan halin yayansa sai yafara bama uztaz hakuri harda hawayensa

Uztaz yace babu komai suka wuce gida suna zaune a falo sai kamall yace sista nazo bisa maganan..... Sai wayar aminu tahau kara yafita yana waya sai sukayi ta jimamin barin raliya gidan sai faisal yace my problem is that nakamu da son Real deeply wallahi banaji kuma bna ganin hanya yanxu damuwata ta ina zan samu wanda yasan inda take sai balkisu tace da kam tna gidan su HASINA but bnsan yanxu ba sai yace gobe xan kokarta naje gidan su Aliyu na bincika but sista idan batanan xuwa nafada yakamani tunda bawani babban gari bane xan iya gano inda take sai yanxu uztaz kabir yace y not bello driver yakaika donshi yasan garin su dama gidansu sosai sai ko hankali Faisal yaji yadan kwanta sukayi sallama ya wucee yatarar da aminu na waya yace muje sai lokacin yace babyna agaida gida da in-law na sai yakashe sai Faisal kallesa yace shegen kaya budurwa kayi  yace eh but xan hada ku da ita sooon yace faiz ina zamuje kuma yace maidani gida kawai muyi hira , yace dawa ???  Faiz yace dakai man yace tab yasin gidansu yer fara xani komuje ne ku gaisa sai faisal yace noh kaini gida kawai kabari akwai abinda nakeyi idan nagama sai akaini mugaisa toh ya sunanta?? Sunant HAA sai ga kira ta yashigo hakan yakatse be karasa furta sunan ba,  yadauka tare da cewa aminci Allah yatabbata agareki yer fara...  can sai yace ok sai nazo swrty byee tkcr plx, sai da sauke wayar ya kalli faisal yamai sigina, sai faisal yace ya toh gayami. Sunanta ??  sai yace nifa sunanta  nada  tsada sai dai in zaka saya?? Faisal ya zaro idanu yace aww abin hakane?  Shiknan yayi shru sai aminu yace karkayi fushi fa... Faisal yayi dariya yace havaa2 akan wan nan ??  sai randa naganta naji daga gareta sai amin u yace yawwwa dayafi ma..... Sai faisal ohhh su el amin da soyayya sai yace ah toh me za a fasa faisal yace mutuwa ko hisabi yace bakodaya sukaci gaba da dariya ya maidashi gidansu sukayi sallama yawucee shikuma yanufi gate zai bude yaji arufe sai yaji muryan kamall nacewa kaje inda kafito ka kwana faisal takaici yamasa yawaaa yadinga rokonsa amman tir yaki  sai yaciro wayansa yakira maamaa yana ta ringing bata dauka, sai yakira binta tadauka yace binta maaamaa tayi bacci ne??  Tace aaa suna falo dasu uwani da kamall sai yace kixo ki bude min gate sai tace toh tana shirin tashiwa faisal ya jiyo muryan maamaa na cewa in har kika bude abqkin aikinki..  ta kwace wayar ta kashe yasake trying switch off....

 Karshe yaga ba shi da tayi yace bari nakira aminu naje gidansu na kwana sai kuma yace kaii bedace na tona asirin gidan mu ba...SAI ya kishingida abakin gate yana ta sake sake a ransa  har bacci yayi awun gaba dashi....
Can misalin 2:30 mai gadi yabude gate sai faisal yaji ana tabasa yace Faisal!  Faisal3 sai yace na.'am yace  ka shigo kowa yayi bacci yatashi yashiga ranan a dakin maigadi ya kwana yna ta ske sake acikin ransa shin ya Zaiyi yatabbata da abba da umma suna nan da haka baza ta taba kasancewa ba.. Wani guntun hawaye ya gangaro mai ya goge da gefen hannunsa yace Umma kinuna mana hadin kai da dan uwana amman ga abinda yake min amman na yafemar umma ALLAH ya fitto mana dakai lafiya dadddy😭😭 yace AMEEEN

Misalin karfe 4:30 yanufi masallaci yayi alwala yashiga masallaci yayi nafil filli san nan yaadaura da karatun Qur'ani....  bayan sallan asubahi ne yaxauna yana ta addu 'O I  sai wajen 7 ya nufi gida yashiga kai tsaye falo yaga bakowa sai ya jiyo hiransu a dakin maamaa sai yanufi can... Yatararr dasu suna hira sai yaxauna ya gaishe su duk suka ammsa amman fiska ba fasaha, sai yace maamaa jiya nafita yaya kamall ya rufe min kofa..  sai tace akan meyasa?  sai yace nima bnsani, sai tajuyo ma kamall tace meyasa kayi  ma dan uwanka haka.   Buda bakin kamall yace maamaa damuka hana sa nema raliya balkisu ya koma SO!  faisal yace azubillah wallahi maamaa bahaka bne balkisu sista nace fa ninaje muyi wani magan........  Uwani ta karba game da raliya ko???  Sai yace Eh bako shakku a tattare dashi,  sai mama tace fita kabani guri SHA-SHA-SHA........

Yanufi kitchen yatarar da binta na aiki tana ganinsa ta fara hawaye tace kayi hakuri yaya faisal wallahi maama......  Sai ya daga mata hannu yace karki damu plxxx kinji naji komai tun jiyan sai tace nagode yace bbu komai taciga da aikinta yace in kin gama breakfast ki kawo min nawa dakina cux inaso nafita sai tace toh....

Yanufi dakinsa yayi wanka ya shirya yana xaune yana karanta wasikar jaki sai binta tayi knocking yace tashigo....  Ta ajiye tire har xata juya yace binta tace na am ta dawo ta durkusa yace  me kikasani game da barin raliya gidan nan,?  Anan ta bashi labarin abinda ya faru tundaga farko harkarshe sai yaja numfashi mai nauyi yace binta kinyadda real xatayi wannan danyen aikin sai tace aaa, sai yace fine datafita ina ta tafi sai tace gidan su hasina sbd daga baya ummar su hasina taxo yi wa maamaa bayani amman taki yarda ta koreta, sai yace ina wayarta fa sai tace yana cikin drower na dakinta tare dawata paper nan kuwa yayi wuff yatashi a xabure... Yace muje suka nufi dakin real ya bude drower yaga wayar daya saya mata kuma ga guntun paper yadauka ya budewa yaga DAFATAN KAI BAZA KA KASANCE CIKIN MASU ZARGI NA BA YAYA FAISAL,?
sai wani hawayen tausayi da so ya gangaro mai ya goge yace baxan taba ba real nasanki wallahi nasanki, sai yanufi dakinsa, yana xaune tunanin duniya ya mai yawaaa kawai yafito yasa akaima facin tayun motansa

Around 11:00 yanufi gidan su ALIYU yana xuwa yatarar da aliyu a bakin gate zai fita ya sauka  su ka gaisa Aliyu na ganinsa xuciyarsa tafara saka mai karkayi sake a kwace maka raliya for second time, sai faisal ya katsar masa da tunani tare da cewa Aliyu naxo muyi magana dakai ne akanraliya sai yanxu aliyu ya sawwko a motarsa yace ina jinka sai yace nazo nabata hak.... Aliyu yace dakata bayan kun wulakanta tan kenann dabadan hasina na gidan ba wayasan yanxu halin datake ciki kuma, bayan nan anbi maamarku a mata bayani amman ta wulakanta min uwa don haka kabar kofan gidan mu kafin ranka.....  ya baci yace bahaka bane ka tsaya ka fahimceni hydar, tuni ya shiga motansa yatayar yama mai gadi horn yace wallahi idan kabar wannan yashiga gida abakin aikinka, jiki na rawa dayake sunsan halin aliyu da xuciya. Ya fixge motan sa ya bar gurin faisal ya rasa nayi wannan shine gasamu kuma ga rashi, har ya shiga motansa xai tafi sai yace xai jira yasake rokonsa ranan a anguwar ya wuni... Gurare la asar sai ga aliyu ya dawoo yasake taransa da magann na ma aliyu yamai kashedin da yabar kofan gidansu.......
Sai da yayi magrib sanan ya bar wajen yana hanya balkisu takirasa 'ina kashiga ne yau kaje gidan su a aliyu anan ya kwashi xance ya zayya na mata' yace meye mafita sista sai tace akwai kazo gida sai nufi gidan su balkisu.... Yana isa yamata waya yace gani naxo sai tace toh ta fito sai yace sista meye mafittan😭 sai tace gobe kaxo ka muje gidansu Aliyu ka parker nesa da gidan tunda ni mace ce xa abarni na shiga namana convincing na real tafito ku hadu sai yaji farin ciki yace nagodee sista i wll never forget u tace u deserved it faisal yace xan koma gida tace aaaaa kashigo kaci abinci nakusa gamawa yace aaa kibarsa sista sai tace to bazani ba yace ehh😳 muje muje zanci suka shiga suna ta dariya

Washe gari misalin tara nasafe faisal yana cikin nishadi  sai ga wayar balkisu tace faisal muna hanyar asibiti jabir ba lafiya yace toh ya kashe ya nufi gidan su yatarar suna shirin fita yabisu har asibiti shiya biya komai da komai na asibitin typoid ne ke daminsa anyi admitting nasa can bayan la'sar sai balkisu da faisal suka fita harabar asibiti suka samu guri suka zauna suna hira, sai balkisu tace ya muje ka kaini don na fuskanci kana cikin  damuwa Faisal, yace aaa kibarsa sai gobee sai tace aaa yau namaka alkawari xan maka ai, sai yace hakane sista but yanxu haka ina mai miki tabbacin aliyu yadawo kuma bazai barki kishiga ba, sai tace havvaa muje kawai...........
Suka nufi gidan suna xuwa faisal yayi parking agun wani masallaci nesa da gida balkisu tasauka ta taka har kofan gida xata shiga sai ga Aliyu na shirin fita suka gaisa yatambaye ta yakowa da kowa?? xata wuce,  yace su hajiyan basa nan sai tace real fa?  Sai yace tare suka fita sai ta juya xata koma yace bazaki shiga kisha ruwa ba tace aaa nagode ta juya shiko yana gurin har ta tafi, ya fada acikin ransa hmm bakin ku daya kuma faisal da raliya sai a dream

Balkisu tazo tasanar da faisal abinda ya awku... Faisal yayi shru chan yace hmmm  bngaya miki ba kuma ina mai tabbacin suna nan amman muje gobe kamar 11:30 haka muxo cux a time din ya fita tace ALLAH yakaimu....
Washe gari tun 10:00 faisal na asibiti acan ma balkisu tasashi yayi breakfast sukayi ta hira wajen sha daya da rabi suka nufi gidan suna zuwa faisal yayi parking akofar gidan sai suka sauka dukansu, Faisal natsaye agun balkisu tashiga.........
Faisal na tsaye sai ga raliya a gaban sa sanye da duguwa riga lemon green tana mai wasa masa murmushi balkisu na tsaye a bayanta itama tana dariya yace alhamdulillah real ashe zan sake ganinki sai tace sosai ma masoyina, najima da gane kana so na kuma nima na amince maka, yace kai ba mafarki nake yi ba ko gixo kike min real......
Tabbas gizo take maka inji balkisu.....  sai yanxu yaga balkisu ita kadaice tsaaye fuskanta ba fara'a tace Faisal mekakeso ka daura wa kanka tunda na fito kana ta surutu kai kadai kamar mara hankali, sai hawaye ya gangaro mai muryansa na shashshakewa yace sisi sista yaa yaamuke ciki sai tace, yau suka nufi gombe...   What 😳 raliya kadai ne??
Sai tace aaaa da ummarsu da hasina da aliyu, abban su ne a gida shima yana shirin zuwa kano yanxu, INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN   abinnda yake ta furtawa kenan yace sista shiga mutafi.... Suna tafiya yana ta sakar zuci sakar so, sukaje asibiti yadaura kansa akan sitiyarin motan yana kuka tamkar yaro karami balkisu tayi ta rarrashin dafadamai maganganu kamar haka (Hava faisal shin bazaka amshi kaddara aduk inda taxo maka ba, kaifa musulmine kuma nasan kayarda dashi kuma ni balkisu ina mai tabbacin kana addu a akan lamarin, tace shin kayi istihara kuwa gameda ita?? Yajuyo idanunsa sun kada sunyi jajur yace sista tun farko danaji son ta araina abinda na fara kenan hakan kuma yasa sai kara sonta nakeji a raina sau uku ina yi amman ba ragi saiii kari uhmmm uhmm sista yaxanyi😭😭😭??
Balkisu kanta sai da tayi hawayen tausayi, tace adduk lokacin da bawa ke neman abu gurin mahalliccinsa idan yana addu a tattara komai zai yi ya miki ma ALLAH........
Faisal yajuyo yace naam sista tace mekake ganin xamuyi yace sista sai ya goge hawayensa, inaga ran friday xan nufi gombe nida bello driver, sai balkisu tace a yanxu haka idan iyayen real sukaji abinda aka mata kana zaton baxasu koreka ba kuma kaga aliyu su suka taimaketa kuma kasan shima yana sonta, sai yace sista wallahi real batason Aliyu kona minty daya xan iya cewa gurbin dana ke dashi agunta shi bayi da ko kwatana,kuma real zata karbeni daga gun iyayenta na fadin bana gari abin ya faru,  sai tace hakane, sai yace sista ki goyamin bayan tafiya ina mai miki tabbacin dawo da raliya gidan nan tace nabaka bros, yace nagodeee ALLAH yabarmu tare tace AMIN tanufi cikin asibiti shikuma yanufi gida


Da daddare yaje yatarar da maamaa yace maamaa inaso naje gombe ran jumma'a sai tace kai da wa yace nida bello tace dawani motar yace nawa sai tace Allah yakaimu..........
Faisal yayi mamakin yadda maamaa takarbi maganan nasa don haka yanufi gurin su bello ya sanar dashi bello yace bakomai oga Allah yakaimu anan suka zauna sukayi ta hira can taran dare yake bello anguwansu Lubbe yadawo yashiga dakinsa yadau wayarsa yakira balkisu sukayi ta hira yace maaamaa fa tafara saukowa tace ALLAH yamana ,yace amin

Ran thursday da zumudinsa yashirya kayan sa, sai yaje fadawa bello akan daya kwana anan don suyi sammako,yana xuwa yaga bello bainan sai yayi tunanin ko sun fita ne sai ya share, can bayan la'sar yasake dubasa be gansa.. Sai yakira wayarsa switch off yaja mota yanufi gidansa sai matarsa tace daxu yaxo yamin sallama ya tafi wudil ya dawo gida yarasa abinyi, yakira balkisu yafada mata tace dole mu jira ko ran saturday ka kama hanya don ban yarda katafi kai daya ba....................

Yasirrr yace wallahi sai na illata ka kai maye ne ka cinye min uwa da kanwa...
Wani yanayin tashin hankali dana shiga yasa nafara ganin bibbiyu,Aliyu yakama hannun yasir yace kabarshi yasir yace baxan barshi ba idan bakasan darajan su ba ni nasani......  Muhammad sai hawaye yana cewa wallahi ni ba maye bane..
Cann umman su hasina ta farfado amman hasina shru, bayan ta dan jinginu aka mika mata ruwa tasha ummansu tace dole hasina ta yi shocked shin fatalwane ko sabb sallaman su umma ya katsar da ita kawai ta mike a firgice ta nuna abbamu da yatsa  tace yaaaa........ Abbana yace rabbb tuni shima yafadi itama haka,,,  Aliyu ya gama kidemewa sai zufa ne ke yanko mar,  ammi sai salati takeyi zam zam sai kuka ummana kuma bata magana shin meyake  faruwa nee doctor kansa ya rikice,sai yanxu aliyu yayi wani ihu yace enough ya isaaa kar muma muhadu da BP don haka munufi asibitin gombe!!!!!!!!!!!!

Yasir mu tafi gombe asibiti yafi duk suka yarda amman Muhammad yace bazashi ba daman anxo ma da yasir mai a galon yace adura mai amman baxai bar Muhammad baa.. Yakamashi damm tamkar barawoo,  baba zuwaira tagudu tagaya wa mai gari akan sun tafi gombe yaxo dakansa yahadamu da dogare biyu da motansa muka nufi gombe,

Muna isa muka nufi miyatti ALLAH hospital wani babban asibiti mai zaman kansa  ba a tsaya wata wata ba akashiga dasu dakin majinyata ana musu dubawan gaggawa, ammi ta dauki wayarta takira mai aikinta tace hello( maraz zaine jibi lena akil nahnu fi lubta hana miyatti ALLAH guli le bala direba ijibiki dakud) ina xaune ina ganin yanda bakinta ke motsi yaren yamin dadi sosai, sai naji zam-zam tace( ammi a nina namshi le bet nakulu wa nalbarrad) sai tace raliya ku tashi kuje kuyi wanka kuci abinci kudawo ni ina nan aliyu da yasir suka ce suma suna nan,sai direba yakaimu gidansu zam zam mukayi wanka mukaci abinci muka dawoo,

Mun dawo dai-dai da doctor yafito yace case nasu is very  easy shocked ne kawai sun ga abinda ya firgitasu sosai , yasir kam nagefe shida aliyu da muhammad,  shikam kansa akasa yana ta hawaye yanayin dana gansa naji tausayinsa yagama dabai bayeni, sai nace Dr umma na da abbana fa cux nasan su hasina da umma ganin Muhammad ne may be sun sanshi a wani guri toh iyayena fa sai yace dukkansu shocked ne sai dai nawani yafi nawani.... but hajiya rabi tafarka xaku iya shiga kanta.........
Bamu tsaya ba sai dakin ina dosa naji tana cewa kukawo min yayana,  yaya kaxo nice, muka shiga aliyu yaje yakama hannun ummansa yace umna meyafaru meyasameki plxxx umma, sai tace raliya kixo yata kawai ta rungumeni takama kuka................... .

Bayan magriba aka sallamemu kowa da magana abakinsa amman kowa ya adana shi domin umma rabi tace batason kowa yayi magana sai an koma gida,muka nufi babban falon Abban su yasir kafin mu iso an shirya mana abinci kala2 mukaci amman sama2 kowa sai kallon kowa yakeyi yasir yayi karfin halin yace kutashi muyi sallan isha mukayi jam i yasir yajamu harda abbansu munyi sallama muna addua sai ga sallamar abban su hasina, kowa yayi mamakin zuwansa muka idar da sallah sai aliyu yace abba ya akayi kaxo yace naji ummanku da hasina ba lafiya shiya nazo u know how much i care fr my family ai, sai hajiya rabi tace nasan xuwanka zai yi amfani sosai...
Sai tayi jimm da kanta akasa sai aliyu yace umma talk mana kinbarmu a duhu sannan kince kar muyi magana, sai tace abban mu sunan datake kiran mijinta dashi kenan sai yace naam, sai tace kasan wannan tanuna shi da hannu, ya kalleshi sosai sannan ya murza idanunsa yace yaya salisu, sai naga abbana yayi murmushi yace naam, sai tace wannan fa sai yace zeenat, sai ta nuna Muhammad, sai yace hmmm hajiya dabadan SABEER yayi accident ya kone ba dasai nace shine

Anan aka zayyana labarin asalin mu kowa sai kuka ashe labarin da hasina ta taba bani labarin iyayaena ne,farin ciki ne ko bakin ciki ne yake sani kuka, sai umma tace bari nakira abba nagaya mai martaba sai, abbansu hasina yace aaaa gobe early in morning mu nufi kano sai sukace toh mukayi addu a muka watse

Washe gari karfe biyar mun dau hanyar kano dukan mu harda yasir da zam zaM amman banda mummy su cuxx sunce sai wani tym din zasu zo, muna tafiya muna ta hira a mota munyi jerin gwano motan abban su hasina agaba matarsa da yayan matarsa da matarsa shima... Anamu kuma siyanan yasirne nida zam zam da a sit na karshe, aliyu da hasina atsakiya muhd da yasir a gaba, motan bayan mu kuma baba zuwaira da fadawa biyu da aka hado mu dasu zasu nufi nafada don sanar wa mai gari, zam zam busy da waya tana karan ta novel na KMag mai suna YAN UBA tace hasina dazaki karanta novel din nan da kinyi kuka, sai tace dan bani nasha mana sai yasir yace kiyi visiting na blog nata mana zaki samu novels na hausa iri iri sai nace toh kawai naji yasir ya tsaya dai dai hanya shiga garin nafada sai nace lafiya yace su umma sun tsaya, muka sawwko shin kunsan wani abin mamaki wai ummu da abbana baxasu kano ba, aka tsaya ana ta basu baki amman ina samm su ba inda xasuje. Munfi awa biyu ana basu baki amman wai su babu inda zasuje, sai yanxu motan fadawa biyu da baba xuwaira suka iso... Hajiya rabi takidime sosai sai abban su hasina yace shiknan kutafi kubi su zuwaira mu xamu wuce da raliya kano sai munemi wanta muje gurin sarki... Sai suka ce sun amince

Muka nufi kano suka wuce nafada,abin yayi mugun tada min hankali ba kadan muna hanya nama yaya garba waya nace mai gamunan xuwa yace  shiknan  sai munxo amman ban bayyana mai abinda ke awwkuwa mun isa la asar liss mukayi gidan yaya garbaa dake Darmanawa tudun fulani, yaya yakarbe hannu tara tara kafin mukayi sallah aka kora mai bayani farin ciki kamar ya suma, amman yanuna bacin ransa da su abba sukaki xuwa don haka bamu tsaya wata wata ba muka nufi gidan mai martaba Inuwa SMS........

Shigan mu harabar gidan naga antaso ana ta mana kirari musamman ma umma rabi (kai ashe haka muke da matsayi ALLAH Mai iko mai yin yanda yaso)abinda nafadi a raina kenan hajiya rabi straight takaimu babban falon Mai martaba inuwa Sms, sallamar mu keda wuya naga wani dattijo mai cike da jazama da kwarjini daka gansa kaga  jinin mahaifina a jikinsa muka isa yace Rabi atul badawiyya zuwa ba sanarwa tace ALLAH RAINE ALLEH DIMA tuba nake, Sai tace inaso ganin ahlil gidan nan domin nagabatar muku da wadan nan baki yace toh bari aka wo muku ruwa kusha......
Iyah kauyenci nayi wato cup na ruwa da aka kawoo mana wani design ne da bntaba gani ba kubartani tashin kauye ko su yasir sai dai sukayi kauyanci cup mutane ne ga ka aba suna zagayewa amma kuma ka leka ciki cup ne woow mukasha ruwa da kayan itatuwa da aka gabatar mana.........


A nijer kuwa fiddy da suhailat antura su wani workshop a gombe, don haka tace sai ta biya abuja before ta tafi...............

Shikuma faisal yana nan yana tsumayen dawowan bello.. Ranan da la'asar yana masallaci bayan sallah yana azkhar, sai ga bello yayi sallama ganinsa ba karamin jindadi yaji ba,  yaxauna kusa dashi yace faisall wallahi inasona kaikai inaso muje tare amman maamaah tace a bakin aikina don haka xan maka taimako daya gobe kaxo da safe gidana na rakaka tasha nasaka a motan nafada, sai na baka adreshin gida kaji yace toh mal bello nagode sosaii ALLAH yasaka da alheri, daya fito yasanar da balkisu abinda sukayi tace shiknan hakan ma yana da kyau.